GWAMNATIN JIHAR KADUNA TA HARAMTA AIKIN BARA, TALLA DA ACHABA

0
848

Daga Usman Nasidi

GWAMNATIN Jihar Kaduna karkashin jagorancin Malam Nasir El-Rufai ta haramta talla, bara da kuma aikin achaba a jihar Kaduna da kewaye.
Gwamnatin jihar Kaduna ta haramta bara, talla, da aikin achaba.
Wannan labaran na fitowa ne bayan majalisar tsaron jihar ta gana a jiya Talata, 8 ga watan Maris a gidan gwamnatin jihar.
Bayan magana da manema labarai, mai magana da yawun gwamna ElRufai, Samuel Aruwa, ya ce an yanke wannan shawara ne domin tabbatar da tsaro bisa ga labaran da aka samu na yunkurin tada tarzoma a jihar.
Ya ce: “Majalisar tsaro jihar Kaduna ta alanta haramcin bara, talla da kuma amfani da Babura wato achaba a birnin jihar Kaduna da kewaye kuma dokar za ta fara aiki yanzu har ranan da Allah ya yi.
“Rahotannin da jami’an tsaro suka samu ne ya wajabta wannan doka. Kana kuma an umurce su da su tabbatar da cewa babu wanda ya saba wa wannan dokar hana bara, talla da aikin babur.
“Saboda haka ana kira ga mutanen jihar su hada kai da jami’an tsaro yayin tabbatar da wannan doka. Babu babur din da za a yarda ya dauki wani fasinja.”
Wannan abu na faruwa ne bayan an alanta cewa za a kulle babban filin jirgin saman Abuja kuma a yi amfani da na Kaduna a madadinshi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here