WATA MATA MAI YARA 6 TA JEFAR DA JARIRINTA A RAMI

0
866

Daga Usman Nasidi

AN kama wata mata mai suna James da ta yar da yaro a cikin rami domin talauci a jihar Bauchi.
Matan ta yi kuka a baban ofishin \’yan sanda a ranar Juma’a bayan da suka nuna ta ga mutane.
Kukan jariri ne ya sa maƙwafta su ka ji suka kuɓutar da shi bayan ya yi wajen sa’o’i 12 a cikin ramin.
Da gudu aka kai yaron baban asibitin Abubakar Tafawa domin duba lafiyan shi.
Matar ta ce ta yar da yaron ne domin rashin wadata bayan mijin ta ya rasa aiki da kuma yanayin tattalin arziki na kasar Najeriya.
Ta ce: “Abubuwar sun yi tsanani, miji na bai da aiki, ya yi hatsari wata uku da suka wuce ya kuma damun mutuntakan shi.
Mijina na asibiti wajen jinya, bamu da abinci da za mu ci, muna mutuwar domin yunwa. Na haifu a gida ne sai na yar da yaron a tsalanga domin ban san yar da zan kula da shi. Ban gaya wa miji na ba dai.”
Kwamishinan \’yan sanda na jihar, Zaki Ahmed, ya ce ana kan binciken al\’amarin amma an kai yaron waje yan kula da mutane acikin asibiti.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here