Dokta Bukar Usman Ya Zama Gwarzon Adabin Hausa

1
1339

Daga Zubair Abdullahi Sada

KUNGIYAR Alkalam ta marubuta Hausa mai dimbin mambobi mawallafa littattafai da take a birnin Kaduna garin Gwamna ta zabo fitaccen mawallafin nan kuma shugaban kungiyar Folklore Association of Nigeria (NSF), Dokta Bukar Usman domin ya karbe lambar karramawa da kwarewa kan \’Adabin Hausa\’ na marigayi Dokta Abubakar Imam.

Dokta Bukar Usman ya karbi wannan lambar ne ta adabin Hausa da aka yi wa lakabi da \’Hikaya\’ a wajen taron ranar marubuta ta duniya da aka gudanar a ranakun 3 da 4 ga wannan wata na Maris, 2017 a dakin taro na gidan Sardauna, wato \’Arewa House\’ da ke Kaduna garin Gwamna.

Da yake karin bayani kan lambar da za a bai wa Dokta Bukar Usman, Uban kungiyar ta Alkalam, Mahmoon Baba Ahmad ya ce, irin wannan lambar karramawa za a rika bayar da ita ne duk shekara ga bayin Allah irin su Dokta Bukar wadanda Allah ya yi masu baiwa kuma suna amfani da ita baiwar suna daukaka adabin na Hausa.

A nasa jawabin godiya ga wannan lambar karramawa ta adabin Hausa da aka ba shi, Dokta Bukar Usman ya ce, ba ya da wata kalma da zai iya nuna farin cikinsa dangane da wannan kyauta, sai dai ya ce, yana matukar godiya da wannan kyauta da \’ya\’yan wannan kungiya ta Alkalam suka yi masa. Allah kuma ya bar zumunci.

Idan ba a manta ba shi dai Dokta Bukar Usman mawallafin littattafan Hausa ne da dama da suka hada da \’Taskar Tatsuniyoyi\’ da \’Tarihin Garin Biu\’ da sauransu. Haka akwai aikace-aikacensa a mujallu da jaridu da kuma laccocin da yake gabatarwa a Jami\’o\’in cikin gida Najeriya da kuma kasashen ketare.

Dokta Bukar mutum ne mai neman ilimomi wanda yake bincikensa bayan ya nuna sha\’awarsa a kan yanayi da tsirrai, kuma wannan ne ya sanya shi zama daya daga cikin manyan manoma a Najeriya.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here