Enugu Rangers Za Ta Karbi Bakuncin Zamalek Ta Kasar Masar

  0
  761

  MUSA MUHAMMAD KUTAMA, Daga Kalaba

  RAHOTANNI da wannan jarida ta samu da dumi-dumi daga cikin yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Enugu Rangers wadda ke buga wasan zakarun Nahiyar Afrika an bai wa kowane dan wasa daga cikin su Dala 730. Kudin guzuri da za su sha ruwa kan hanya a ranar Alhamis ta makon jiya ce aka ba su kudin kuma suka kama hanya zuwa kasar Masar domin karawa da kungiyar wasan kwallon kafa ta Zamalek da ke kasar Masar.

  A ranar ne suka tashi daga filin jirgin saman kasa da kasa da ke garin Enugu a jirgin kamfanin kasar Habasha ana sa rai sun isa Masar a ranar Juma’a, sannan a washegari Asabar kuma suka fito filin wasa domin fafatwa da Zamalek .

  Wani  daga cikin yan wasan ya  tababtar da korafin sun a cewa “mu fa har yanzu da sauran rina a kaba domin muna bin bashin alawus din Dalar Amurka 730 da muka je wasa waje da kungiyar JS Saoura.”inji dan wasan da bai so a ambaci sunansa . Za a yi fafatwar tsakanin kungiyopyin biyu ne a filin wasa na Borg El-Arab Stadium da ke birnin Alexendria.kana kuma kuma kungiyar Enugu rangers ta karbi bakuncin Zamalek 17 da 19 ga watan da muke ciki.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here