Buhari Ya Karɓi Ragamar Mulkin Najeriya A Hannun Mataimakinsa

0
7396
Rabo Haladu Daga Kaduna

SHUGABA Muhammadu Buhari zai bi sannu a hankali wajen ci gaba da harkokin mulki bayan komawarsa Najeriya daga jinya
Shugaban kasa  Muhammadu Buhari ya koma bakin aiki tun jiya Litinin, bayan ya shafe kwana hamsin yana jinya a London.
Da safiyar ranar Juma\’ar da ta gabata ne, shugaban ƙasa ya koma gida, sai dai ya ce mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo zai ci gaba da tafiyar da al\’amura a ranakun ƙarshen mako.
Mai magana da yawun shugaban, Garba Shehu ya ce gabanin ya shiga ofis, Muhammadu Buhari zai aika wasika ga majalisar dokokin kasar don shaida mata komowarsa gida da kuma karbar mulki a hukumance.
Ya ce suna fata shugaban zai bi a hankali bayan jinyar da ya yi ta tsawon kwana hamsin.
A cewarsa shugaba Muhammadu Buhari zai ɗan ɗauki lokaci wataƙila kafin ya iya ci gaba da aiki wurjanjan kamar yadda ya saba yi a baya ba.
Wasu \’yan Nijeriya dai sun yi ta bayyana cewa harkokin mulki sun fi kyautatuwa lokacin da mataimakin shugaban, Farfesa Yemi Osinbajo yake riko.
Shi dai Osinbajo ya rika kai ziyara zuwa sassan ƙasa da kuma ɓullo da wasu matakai waɗanda ake ganin sun taimaka wajen farfaɗo da darajar Naira.
A tsawon lokacin rikon, Nijeriya ta ga raguwar fasa bututan man fetur a yankin Naija Delta mai arziƙin man fetur.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here