MAJALISAR DATTAWA DA DSS BA SU ISA SU HANA NI YAKI DA RASHAWA BA – Inji Magu

0
850

Daga Usman Nasidi

MUKADDASHIN shugaban hukumar hana almundahana da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC, Ibrahim Magu, ya lashi takobin ci gaba da yaki da rashawa.
Ya jaddada cewa rahoton hukumar DSS a kan shi wanda ya hana majalisar dattawa tabbatar da shi ba zai hana shi ci gaba da yaki da rashawa ba.
Magu ya bayyana hakan ne yayin da ya yi hira da \’yan fafutuka a kofar majalisan dokokin tarayya.
“Abin da na mayar da hankali kai shi ne yaki da rashawa. Rashin tabbatar da ni bai canza komai ba. zan ci gaba da aiki ko sun tabbatar ko sun ki.
“Ba za mu taba kasa a gwiwa ba saboda muna kokarin binciken abin da mutane suka yi saboda rayuwar yaranmu da tattabakunnanmu. Idan muka ki yaki da rashawa, babu rayuwa ga yaran mu.
“Saboda haka, wajibi ne mu tashi daga barci, duk inda kake, ka yi yaki da rashawa kuma duk lokacin da kuka gano na yi rashawa, ka tona ni.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here