\’YAN SANDA SUN DAMKE WASU MASU GARKUWA DA MUTANE A ZARIYA

0
1015
Daga Usman Nasidi
A ranar Juma’a , 17 ga watan Maris, hukumar \’yan sanda ta ce ta damke yan garkuwa da mutane a garin Zariya, Jihar Kaduna.
Kakakin hukumar yan sanda, Jimoh Moshood ya ce masu garkuwa da mutanen su ne Nuhu Fulani, 32; Yahaya Muhammed, 26 da Aisha Bature, 23.
Moshood ya ce: “Masu garkuwa da mutanen sun kasance kan jerin sunayen wadanda ake nema. Yayin bincike, sun tona asirinsu cewa su ne suke gudanar da sace-sace da kuma garkuwa da mutane a babban titin Zariya zuwa Kaduna.”
A cewarsa, yan barandan sun yi bayani ga masu binciken \’yan sanda cewa akwai wasu rawa da suka taka wajen wasu laifuka a jihar.
\” Kana wasu mutane sun gane su. Amma ana gudanar da bincike a kansu da kuma sauran yan kungiyan da suka arce,”
Daga cikin abubuwan da aka kwace a hannunsu sune AK 47, karamin bindiga, harsasai da waya Samsung S6.
An kama bindiga AK 47a cikin bayin wata Aisha wacce itace matar shugaban yan fashin.
  •  

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here