JIBWIS Za Ta Kaddamar Da Gidauniyar Neman Gudunmawar Sayen Motoci Da Kayayyakin Aiki A Abuja

0
1008
  Isah Ahmed, Jos
KUNGIYAR Jama\’atu Izalatil Bid\’ah Wa\’ikamatis Sunnah ta kasa za ta
gudanar da gagarumin taron kaddamar da neman gudunmawar kudi naira
miliyan 175 don sayen motoci da kayayyakin aiki, a ranar Lahadin nan
mai zuwa a babban birnin tarayya Abuja.
Taron wanda mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa\’ad Abubakar III zai
shugabanta, ana sa ran shugaban kasa Muhammad Buhari zai kasance
babban bako na musamman. Har ila yau ana sa ran shugaban majalisar
dattawa Abubakar Bukola Saraki da tsohon mataimakin shugaban kasa
Alhaji Atiku Abubakar da wakilan shugaban majalisar wakilai ta tarayya
Honarabul Yakubu Dogara da gwamnonin jihohi da dama za su kasance daga
cikin manyan bakin da za su halarci wajen wannan taro.
Hakazalika minintan Abuja Alhaji Muhammad Musa Bello zai kasance
babban mai masaukin baki, a yayin da tsohon gwamnan jihar Neja Alhaji
Mu\’azu Babangida Aliyu zai kasance babban bako mai jawabi. Shugaban
majalisar malamai na kasa na kungiyar Sheikh Muhammad Sani Yahya
Jingir zai kasance uban taron.
Rassan kungiyar na jihohi ne za su kasance manyan masu kaddamarwa, a
yayin da manyan \’yan kasuwa da manyan \’yan siyasa da manyan ma\’aikatan
gwamnati daga sassa daban-daban na kasar nan za su rufa masu baya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here