MAJALISAR WAKILAI TA GARGADI SHUGABA BUHARI KAN KARIN WA\’ADIN MULKI

1
1639
Daga Usman Nasidi
MAJALISAR wakilan Najeriya a ranar Talata, 21 ga watan Maris ta zargi shugaba Muhammadu Buhari kan saba wa kundin tsarin mulkin kasar wadda ya sha alwashin tabbatar da shi.
\’Yan majalisar sun yi wannan furuci ne lokacin da shugaban ma’aikata na kasa, Misis Winifred Oyo-Ita ta bayyana cewa fadar shugaban kasa ta kara tsawaita wa’adin sakatare na dindindin mai ritaya, Dokta Jamila Shu\’ara da shekara daya (har 2018).
Kwamitin ta kirawo shugaban ma’aikata na kasa bayan zargin karin tsawon aikin Dokta Jamila Shu\’ara wanda wa\’adin aikin ta kare a watan Fabrairu 17, 2017 da ta gabata.
Shugaban wanda ta bayyana a gaban kwamitin, ta bayyana cewa ta samu wasikar karin shekara guda a wata wasikar da shugaban ma’aikatar fadar shugaban kasa, Abba Kyari ya isar a ofishin ta.
Oyo-Ita ta kara da cewa wasika mai kwanan watan Maris 7 ga shi, inda aka sanar da ita cewa shugaba Muhammadu Buhari ya amince da karin tsawo aiki na Dokta Shu\’ara da karin shekara daya.
Amma \’yan majalisar sun yi Allah wadai da karin tsawon wa’adin aikin da kuma amince da cewa al’amarin ta saba wa kundin tsarin mulki na sabis.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here