AN SAMU TASHIN GOBARA A OFISHIN HUKUMAR ZABE TA KASA

0
799
Daga Usman Nasidi
AN samu wata \’yar karamar gobara a hedkwatar hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta a Abuja, a ranar Litinin, 27 ga watan Maris din nan.
Rahotonni sun bayyana cewa wutar ta fara ne daga AC na ofishin mai taimka wa shugaban hukumar INEC.
Game da cewar rahoton, wutar ta fara ne misalin karfe 12:10 na rana kuma ta kona labulen ofishin amma da wuri jami’an kashe wuta suka kawar da gobarar kafin ta fara ci sosai.
Idan za a iya tunawa hukumar INEC ta dakatar da ma’aikatanta guda 202 wadanda hukumar hana almundahana da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta ke tuhuma da amsar cin hancin Naira Biliyan 23 (N23bn) a hannun tsohuwar ministan mai, Diezani-Alison Madueke.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here