An Yanka Ta Tashi A Shari\’ar Tsohon Gwamnan Adamawa

0
918

Muhammad Saleh, Daga Yola

A wani hukunci mai kama da wasan kwaikwayo wata babbar kotun jiha, ta bada belin tsohon gwamnan jihar Adamawa Baresta Bala James Nggilari, bisa dalilan rashin lafiya.

To sai dai kallo ya koma sama sakamakon gano takardar da ke nuni da cewa tsohon Gwamnan ba shi da lafiya ta boge ce, bayan babban alkalin kotun Mai Shari’a Nathan Musu ya bada belinsa.

Yadda lamarin ya faru kuwa shi ne; babban jami’i mai kula da fanni lafiya a gidan yarin da tsohon Gwamnan ke tsare SOP Jonh Bukar, ya rubutawa kotun ranar 23/3/2017 cewa tsohon gwamna, yana fama da ciwon hawan jini da bugun zuciya.

To sai dai shugaban gidajen yarin jihar CP Peter Tenkwa, ya ce bashi da masaniyar rubuta waccer wasikar da aka aike wa kotun, ya ce sam a matsayinsa na shugaban hukumar gidan yarin da kuma hedikwatar hukumar a Abuja ba su da masaniya game da wasikar kwata-kwata.

Shugaban ya ci gaba da cewa abune mai wahala da daure kai a ce an rubuta irin wannan wasikar game da wannan shari’a ta tsohon Gwamna ba tare da masaniya ko umurninsa ba, ya ce akwai wani abu, ruwa ba shi tsami banza.

Ya ce tuni hedikwatar hukumar gidajen yari da ke Abuja, ta bashi umurnin daukar mataki a kan wadannan jami’an hukumar biyu da ke da hanu a cikin lamarin.

Ya ce wani abun mamaki babu wani abu na magani da suka rasa a gidajen yarin jihar, ya ce ko ranar Juma’ar da ta gabata an kawo karin wasu magunguna sun raba a gidajen yarin jihar.

Haka shi ma da yake maida kalami game da wannan batu Kwamishinan ma’aikatar shari’a ta jihar Adamawa, kuma babban lauyan gwamnatin jihar Barista Bala Silas Sanga, ya ce hukuncin da kotun ta yanke tamkar wasan yara ne.

Ya ce sam ba a bi duk ka’idojin da ya kamata ba amma aka ce an bada belin wanda kotu ta samu da laifi da daure shi, ya ce hukumar gidan yarin ta rubuta masa wasika ranar 24/3/2017 cewa tsohon Gwamna Nggilari yana cikin koshin lafiya.

Ya ce mutumin da aka tabbatar musu yana cikin koshin lafiya ne kuma aka kawo wa kotu wata takardar ta daban cewa ba shi da lafiya? Ya ce ba su yarda ba, za su daukaka kara kuma za su gudanar da binciken inda takardar ta fito.

Dama dai kotun ta daure tsohon Gwamna Bala James Nggilari, shekara biyar a gidan yari ne bisa samun shi da laifin rashin bin ka’idar da doka ta tsara kafin bada kwangila, a lokacin da yake a matsayin gwamnan jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here