YARONA YA FARA KISAN KAI TUN YANA DAN SHEKARA 12 – Inji Mahaifiyar Dan Fashi

0
757
Daga Usman Nasidi
MAHAIFIYAR wani babban dan fashin da aka kashe, Henry Onyekachi Chibueze, wanda ya fi shahara da suna Vampire, ta ce shaidanin yaro ne kuma da ma ya addabe su a dangi.
Uwargida Beatrice Chibueze ta bayyana wa \’yan jarida cewa yaronta ya fara kisan kai tun yana dan shekara 12 a makarantan firamaren Umuokpu Community, lokacin yana aji 4.
Vampire dai ya rasa ransa ne a ranar 2 ga watan Maris, a dajin Umuuowa a karamar hukumar Ikwerre a jihar Ribas yayin da wata rundunar \’yan sanda ta musamman ta je farautarsa.
Mahaifiyar ta ce: “An haifi Henry Onyekachi Chibueze a shekarar 1981 kuma marigayi mijinta ya sa shi a makarantanr firamare a Umuokpu a Abaja, amma ya fita daga makaranta a aji 5 bayan ya kashe wani abokin sa yayin da suke fada yana dan shekara 12.
“Wannan abu ya tayar da hankali a danginmu har sai da mahaifinsa ya biya diyya don Henry ya kasance yana halayya kaman wanda aka tsinewa.
A cewarta, lokacin da ya bar makarantan firamare, ya ki koyan kowane aikin hannu, kawai sai ya fara bin \’yan iskan unguwa inda ya fara fashi da garkuwa da mutane.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here