ZAN YI MURABUS DAGA KAN KUJERATA IDAN NA GAZA CIKA ALKAWARI – Inji Minista Sirika

0
733
Daga Usman Nasidi
MINISTAN sufurin jiragen sama, Hadi Sirika ya bayyana cewa idan har ba a kammala aikin filin jirgin Abuja ba cikin lokacin da aka dauka zai ajiye aikin.
An dai dauki makonni 6 domin gama aikin hanyar jirgin wanda Ministan ya ce idan ya gaza cika wannan alkwarai da ya dauka zai yi murabus.
Sanata Sirika ya ce ba zai iya zama cikin kunya ba bayan ya saba alkawarin da ya shafi miliyoyin mutane duk da kimanin makonni uku kenan da suka wuce da koma sauka kasar ta filin jirgin Kaduna.
Minista Hadi Sirika ya zagaya tare da Ministan yada labarai, Lai Mohammed domin ganin aikin da ake yi.
Sannan kuma Sakataren gwamnatin tarayya Babachir David Lawal ya wanke kansa daga duk wani zargi da ake yi masa na cewa ofishinsa ya bada wasu kwangiloli ga kamfanin karya wanda aka yi gaba da wasu makudan kudi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here