Ya Bukaci \’Yan Majalisar Dattawa Su Bar Buhari Ya Yi Wa Al\’ummar Nijeriya Aiki

0
738
Isah Ahmed, Daga Jos
SHUGABAN kungiyar masu shayi ta kasa Alhaji Shu\’aibu Abubakar ya yi kira ga \’yan majalisar dattawa ta Nijeriya  su bar shugaban kasa, Muhammad Buhari ya yi wa al\’ummar Nijeriya ayyukan raya kasa da ya sanya a gaba.  Alhaji Shu\’aibu Abubakar ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake zantawa da jaridar GTK, kan dambarwar da ke faruwa
tsakanin majalisar dattawa da fadar shugaban kasa.
Ya ce  \’yan Nijeriya sun zabi \’yan majalisar dattawan ne  domin su je su yi masu  yiwa ayyukan da suka da ce. Ya ce  ba damuwar talakan Nijeriya ba ne su je suna  maganar sanya kakin hukumar kwastan,  abin da ya dami talakan Nijeriya shi ne tsadar rayuwa.
Don haka ya yi  kira ga \’yan majalisar  su bar shugaban kasa ya gudanar da ayyukan da ya sanya a gaba. Su ma su yi aikin da aka tura su yi.
Ya yi kira ga  shugaban kasa ya dauki matakai na yin maganganu a kowanne lokaci, saboda yana ganin shirun da yake yi, shi ya sa wasu masu adawa da gwamnati suke samun dama suna yin abubuwan da suka ga dama.
Ya yi kira ga \’yan Nijeriya su ci gaba da yi wa shugaban kasa addu\’a Allah ya ba shi nasara kan abubuwan da ya sanya a gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here