ZA MU KAMA DUK WANDA MUKA KAMA DA RASHIN GASKIYA – Hameed Ali

0
838
Daga Usman Nasidi
SHUGABAN Hukumar Kwastan na kasa ya bayyana cewa karshen duk wani mugun iri da bata-gari a Hukumar ya zo don kuwa ba zai sassauta ba.
Kanar Hamid Ali mai ritaya ya bayyana cewa duk wanda aka samu da laifi a gidan kwastan din ba zai ji da dadi ba. Hamid Ali ya ce za a hukunta duk wani ma’aikaci da aka samu da rashin gaskiya kamar yadda doka ta tanada.
Hamid Ali yake cewa zai yi kokari wajen hana fasa kauri sannan kuma ya nema wa kasar kudin shiga. Kanar Ali ya gargadi ma’aikata da su guji yin ba daidai ba wajen duba kayan da aka shigo da su cikin kasar.
Kungiyar ANLCA sun koka da yadda ake samun cudani wani lokaci tsakanin hukumar kwastam da sauran hukumomi kamar ‘yan sanda wanda suka ce hakan na ba su matsala wajen shigo da kayan da suka sayo zuwa cikin kasar.
Kwanaki Hamid Ali ya bayyana cewa aikin nasa ba abu ne mai sauki ba tun farkon hawan sa har zuwa yanzu. Hamid Ali ya ce ya iske wasu manya ‘yan kasuwa da ke shigo da kaya daga kasar waje da suka yi kane-kane kan dokokin kasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here