Takaddamar Shari’ar Gwamna: An Hukunta Wasu Jami’an Gidan Yari Biyu A Yola

0
839

Muhammad Saleh, Daga Yola

HUKUMAR da ke kula da gidajen yari ta kasa (Nigerian Prisen Servece) ta hukunta wasu jami’anta biyu a gida yarin Yola da ke jihar Adamawa, saboda  zargin suna da hannu a takaddamar da ta biyo bayan belin da wata babbar kotun jihar ta baiwa tsohon gwamna Bala James Nggilari.

Shugaban hukumar kula da gidajen yari ta jihar CP Peter Tenkwa,  ya shaidawa manema labarai a Yola cewa hukunta jami’an biyu, DCP Abubakar Abaka, mai kula da gidan yarin ya kuma bayyana a hedikwatar hukumar dake Abuja, sai kuma John Bukar jami’i mai kula da kiwon lafiya a gidan yarin da aka tsare shi a gidan kasun.

CP Peter Tenkwa ya ce fitar da tsohon gwamna Bala Nggilari, daga gidan yarin kwana biyu bayan bada belinsa lamarin ya yi kama da almara, saboda dabarar aka yi amfani da ita na fitar shi ta barauniyar hanya.

“yadda aka fitar da tsohon gwamna Bala Nggilari daga inda ake tsare da shi ya yi kama da almara, bisa la’akari da kwarewar da aka nuna wajen fitar da shi ta barauniyar hanya”.

Dama dai daya daga cikin lauyoyin tsohon gwamnan Baresta Obed Wadzani, yace hujjojin da suka gabatar wa kotu yasa kotun ta bada belin tsohon gwamman, amma ba batun takardan da hukumar gidan yari ta aikewa kotu ba.

Akwai dai rahotannin da’a tantance ba da suke cewa tsohon gwamna Bala Nggilari, tuni ya tsallaka zuwa makwabciyar kasar nan wato  Jamhuriyar Kamaru.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here