Kwastan Ta Kama Motoci 7 Maakare Da Haramtacciyar Shinkafa

0
951

Mustapha Imrana, Daga Kaduna

BABBAN jami\’in hukumar kwastan mai kula da jihohin Kaduna da Katsina Kwantirola Muhammad Tanko, ya bayyana cewa \’yan fasa-kwaurin da ke da kunnen kashi sun rikice ne lokacin  da suka tsinci kansu an zagaye su

Sakamakon hakan, nan take suka rika hada kansu da juna a kokarinsu na samun hanyar tserewa.

\” Mun samu nasarar kame dukkan motocin bakwai dauke da haramtacciyar shinkafar da aka yi fasa-kwauri\”.

Amma kwantirolan ya musanta batun yin harbi ko batun kisan kai.

\”Tuni aka dauki lamarin zuwa wajen \’yan sanda kuma wadanda suka ji rauni an dauke su zuwa asibiti suna karbar magani kuma da zarar sun samu sauki za a gabatar da su gaban kuliya\”.Inji kwantirola Muhammad.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here