GWAMNATI TA DUBA MATSALOLIN DA FULANI MAKIYAYA SUKE FUSKANTA A NIJERIYA-SALE BAYARE

  0
  849
  Isah Ahmed, Jos
  ALHAJI Sale Bayare shi ne  Sakataren kungiyar ci gaban al\’ummar Fulani a Nijeriya  ta  Gan Allah. A wannan tattaunawa da ya yi da wakilinmu kan matsalolin da suke damun al\’ummar fulani makiyaya a Nijeriya.  Ya
  bayyana irin matsalolin da suke damun al\’ummar fulani makiyaya a Nijeriya kuma ya bukaci gwamnatin tarayya ta duba matsalolin, domin ta magance su. Ga yadda tattaunawar ta kasance:-
  GTK: A matsayinka na Daya daga cikin shugabannin al\’ummar a Nijeriya, mene ne za ka ce dangane da irin matsalolin da suke damun al\’ummar fulani a Nijeriya?
  Sale Bayari:  Tun muna yara shekaru kamar 30 da suka gabata manyanmu sun gaya mana cewa akwai lokacin da zai zo, da za a sami fitintinu tsakanin makiyaya da manoma. Saboda gwamnatin Njeriya bata tanadarwa da al\’ummar fulani makiyaya komai ba, duk da yawan da suke da shi a Nijeriya.
  kuma  sai muka dago cewa maganar rayuwar fulani a Nijeriya tana son ta zama tarihi.  Ba mu yi mamaki ba kan wannan kunci da al\’ummar fulani suka shiga a Nijeriya ba. Wannan al\’amari yana tayar da hankalin al\’ummar fulani, domin duk wata al\’umma da ta gano cewa rayuwarta za ta zama tarihi a cikin kasa, saboda halin kunci da  musgunanawa da ake yi mata, babu shakka za ta tashi tsaye ta kare kanta.
  A cikin \’yan shekarun nan mun lura cewa, tashe-tashen hankula wadanda suke da alaka da addini da kabilanci da banganranci sun addabi al\’ummar fulani a Nijeriya.
  Tashe tashen hankulan nan sun fara faruwa ne tun a shekara ta 1999, wato lokacin da aka dawo mulkin dimokuradiyya a Nijeriya.  A cikin shekaru 8 da tsohon shugaban kasa Obasonjo ya yi yana mulki da shekaru
  6 da Goodluck Jonathan ya yi yana mulki a kasar nan.  A cikin shekaru 2 nan na gwamnati APC, wato mulkin Buhari tashe tashen hankulan  da al\’ummar fulani suka shiga  sun nunka  wadanda suka shiga a zamanin gwamnatocin  Obasanjo da Goodluck Jonathan.
  Wannan abu yana tayar mana da hankali kwarai da gaske, kuma muna nan muna nazari kan dalilan da suka sanya  gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi da kananan hukumomin kasar nan, suka kasa tabuka wani abu kan rayuwar al\’ummar fulani a Nijeriya.
  GTK: Kamar wadanne irin matsaloli ne al\’ummar fulani suka shiga a cikin wadannan shekaru 2 da kace sun ninka matsalolin da suka shiga a zamanin gwamnatocin Obasanjo da Jonathan?
  Sale Bayare: A shekaru 14 na gwamnatocin Obasanjo da Jonathan da suka gabata. Ba taba cewa za a kori fulani a hana su kiwo  ba, sai a wannan lokaci.
  Tun daga lokacin Annabi Musa wanda ya fara kiwo a duniya, har ya zuwa yau  bafulatani bai taba tunanin cewa za a zo a gaya masa ba zai sami hanyar da zai je ya ciyar da shanunsa da ciyawa da ruwa ba, sai a wannan lokaci.
  A yanzu duk inda ada fulani suke zuwa su shayar da dabbobinsu ruwa ya zama wuraren yin lambu. Duk inda suke bi  wato burtali yanzu ya zama gonaki.
  Aka zo ana cewa wai za a yiwa fulani wuraren kiwo a lokaci guda kuma manoman kasar nan, suka ce ba zasu yarda a dauki gonakinsu a mayar wuraren kiwon dabbobi ba.
  Saboda haka gaskiyar magana dole gwamnati ta tsaya ta lura da halin da al\’ummar fulani makiyaya suka shiga a Nijeriya. A  kasafin kuxin da ake yi wa harkokin noma a Nijeriya, ba a yiwa fulani  makiyaya komai.
  Duk maganganun da ake yi kan harkokin noma a Nijeriya ana maganar takin zamani  da taraktocin noma  da irin shuka da magungunan feshi ne kawai. Ba a maganar makiyaya da dabbobinsu.
  Saboda kowa yana cin nama da araha a Nijeriya ba a shigo da naman shanu da awaki da tumaki daga kasashen waje. Saboda haka muna son gwamnatin Nijeriya ta gaya mana ta yaya ne ake son makiyaya su yi
  rayuwarsu a Nijeriya?
  Yanzu a Nijeriya kowa yana da yanci ya tafi duk inda ya ga dama ya zauna, amma banda fulani makiyaya. Misali kwanan gwamnan jihar Benuwai Sameul  Ortom ya fito ya ce fulani suna da \’yanci su yi kiwo a ko ina a Nijeriya, amma a jihar Benuwai babu wurin kiwo. Bayan tsarin mulkin Nijeriya ya ce duk dan Nijeriya yana da \’yancin ya shiga ko ina a Nijeriya ya zauna,  babu wanda ya isa ya hana shi zama.
  Tun kafin a san za ayi Nijeriya fulani suke a jihar Benuwai, domin tarihi ya nuna mana fulani sun fi shekaru 750 a jihar Benuwai.
  Babbar matsalar da take damun al\’ummar fulani  a Nijeriya ita ce ana son a nuna masu cewa kiwo ba zai yuwu ba a Nijeriya. Kuma gaskiyar magana babu inda aka hana kiwo a duniya. Ko a Amerika har yanzu ana yin kiwo akwai cowboy suna nan suna hawa dawakai suna bin shanunsu tun daga New Mexico har ya zuwa Calfornia, suna  tafiya ta wajen kilo mita dubu 5 suna bin shanunsu.
  A nan Afrika kamar Kenya da Cango da Ruwanda da Burundi da Sudan ta kudu fulani suna yawo da shanunusu.
  Abin da ke damun bafulatani  a Nijeriya  \’yayansa basu bar shi ba, jami\’an tsaro da alkalai basu bar shi ba. Sannan ana ana yin garkuwa da fulani a daji ga kuma matsalar barayin shanu.
  Kuma abin bakin ciki akwai wasu kungiyoyin fulanin wadanda  aikin su shi ne satar shanu. Irin wadannan kungiyoyi suna  da wuraren  karvar shanun sata a garuruwan Legas da Asaba da Oka. Wallahi akwai kungiyoyin fulani a kudancin Nijeriya shugabanninsu barayi ne.
  GTK: To a nan wadanne matakai ne wannan kungiya ta Gan Allah ta dauka kan magance wadannan matsaloli, musamman matsalar sace sacen shanu?
  Sale Bayari: Wannan kungiya ta Gan Allah ta dauki matakai da dama kan magance matsalar sace sacen shanu a Nijeriya. Sakamakon matakan da muka dauka ya sanya barayin shanu a Nijeriya, suna kiran  wannan kungiya EFCC saboda sun gano cewa mun sanya masu ido.
  GTK: Karshe wanne sako ko kira ne kake da shi zuwa ga gwamnati?
  Sale Bayari: Muna kira ga gwamnatin tarayya ta sani cewa akwai babban hadari a gabanta  ace  ba a san yadda za ayi da fulani makiyayan Nijeriya ba. Fulani makiyayan Nijeriya sun fi mutum miliyan 20 kuma mutanen da suke cin abinci a kan wannan harka ta kiwo sun fi mutum miliyan 20, don haka a lokaci daya ace  za a datsa hanyar cin abincin wadannan mutane akwai hadari. Muna son gwamnati ta san abin da za ta yi a kan wannan al\’amari.
  Kuma muna son gwamnatin tarayya ta kafa wata ma\’aikata ta fulani makiyaya a Nijeriya wadda zata kula da matsalolin al\’ummar fulani makiyaya a Nijeriya.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here