Hukumar EFCC Ta Sake Wawan Kamu.

0
868

Rabo Haladu Da Usman Nasidi Daga Kaduna

HUKUMAR hana yi wa tattalin arzikin Nijeriya ta\’annati EFCC ta sake kama wasu maƙudan kuɗi sakamakon kwarmaton masu fallasa bayanai suka yi a ranar Litinin.

Jami\’an EFCC sun kama kuɗin da suka ƙunshi kuɗaɗen kasashe daban-daban a fitacciyar kasuwar Balogun da ke Lagos.
Mai magana da yawun hukumar, Wilson Uwujaren ya ce kudin sun ƙunshi Yuro dubu 547 da 730 da kuma Fam dubu 21 da 90 da kuma Naira Miliyan biyar da dubu 648 da 500.
Jimillar kudin ta kai kimanin Naira Miliyan 250.
Kamen ya biyo bayan tsegunta wa hukumar EFCC ne game da wasu mutane da ba a bayyana sunayensu da suka yi safarar kimanin Naira Miliyan 250 zuwa kasuwar Balogun don canza su.
\’Yan canjin da aka kama kudin a wajensu sun ce wani ubangidansu ne ya aiko musu da kudin don canzawa.
EFCC ta ce mutum biyu da ta kama suna taimaka mata a binciken da take yi.
A ranar Asabar cikin makon jiya ma, hukumar EFCC ta ce jami\’anta sun kama maƙudan kudi a wani babban shago a birnin Ikko.
Wata sanarwa da EFCC ta wallafa a shafukanta na sada zumunta ta ce jami\’anta sun gano sama da Naira Miliyan 448 yashe a cikin shagon, wanda aka dade ba a buɗe ba, bayan an tsegunta mata cewa ana shirin canza kuɗin.
A cewar EFCC, shagon na da tambarin \’yan canji, amma an shafe sama da shekara biyu ba a bude shi ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here