Mun Sayar Wa Kamfanoni Masara Da Waken-soya Na Miliyoyin Naira A Yankin Saminaka-Bello Saminaka

0
823
Isah Ahmed, Jos
SHUGABAN kungiyar saye da sayar da masara na karamar hukumar Lere da ke Jihar Kaduna, Alhaji Bello Aminu Saminaka ya bayyana cewa a bana sun sayar wa da kamfanoni masara da waken soya na Miliyoyin naira a yankin
Saminaka. Alhaji Bello Aminu Saminaka ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu.
Ya ce  na farko sun sayar wa kamfanin Grand Cereals da ke Jos waken soya na kudi sama da  naira biliyan  1. Ya ce bayan nan sun sayar wa wannan kamfani na Grand Cereals masara.
Alhaji Bello Aminu ya yi bayanin cewa a kashin  farko sun sayar wa wannan kamfani  masara tirela 450.  Sannan kuma a kashi na biyu suka sake sayar wa wannan kamfani  masara tirela 130.
\’\’Bayan haka mun sayawa kamfanin Apex da kamfanin Premier masara. A kashin farko  mun sayar wa kamfanin Apex  masara tirela 100. A kashi na biyu, mun saya masu masara tirela 250.  Bayan haka akwai kamfanin
fulawa na Golden dake Kano suma sun zo wannan yanki sun sayi masara.
Akwai kamfanin fulawa na Kaduna suma sun zo wannan yanki sun sayi masara. Akwai wasu kananan kamfanoni da masu gidajen kaji da suka zo wannan yanki suka sayi masara, kamar tirela 5 zuwa 10 a wannan yanki\’\’.
Ya ce a  gaskiya  bana manoman wannan yanki sun ji dadi  yadda aka zo aka sayi kayayyakin amfanin gona a wannan yanki.
Ya ce yanzu kauyukan wannan yanki mutane suna ta gine ginen gidaje suna buga kwano. Saboda arzikin da Allah ya kawo masu sakamakon noman da aka yi a wannan yanki.
Alhaji Bello Aminu ya nuna damuwarsa kan yadda gwamnati ta bari aka shigo da masara a kwanakin baya. Ya ce idan aka ci gaba da shigo da abinci kasar nan, za a karya wa manoman kasar nan gwiwa. Don haka ya yi kira ga gwamnati kada ta yarda da \’yan bani na iya su sanya ta amince a ci gaba da shigo da abinci cikin kasar nan. Domin za a iya noma abincin da za a ci a nan gida Nijeriya.
Daga nan ya nuna goyan bayansu ga shirin a koma gona na gwamnatin shugaban kasa Muhammad Buhari. Ya yi kira ga manoma su kara zage damtse su ci gaba da rungumar aikin noman nan da suka sanya a gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here