MUTUM 3 SUN MUTU, DA DAMA SUN RAUNUKA A RIKICIN SOJI DA \’YAN SANDA A DAMATURU

0
897
Daga Usman Nasidi
AN yi wata mummunar arangama tsakanin sojoji da yan sanda a garin Damaturu babban birnin Jihar Yobe wanda rikicin ya yi sanadiyar mutuwar mutane uku yayin da da dama suka ji raunuka
Al’amarin ya afku ne a cikin wannaan makon na watan Afrilu lokacin da sojoji da yan sanda ke musayar wuta a garin Damaturu babban birnin jihar Yobe wanda ya zamo filin yaki yayin da sojoji da \’yan sanda suka kara.
Farar hula sun ci na kare tare da yan kasuwa maza da mata inda suka bar kayayyakin cinikin su a yashe a kan tituna don tsirar da rayuwarsu.
Yakin wanda ya afku tsakanin hukumomin tsaro biyu, ya sanya komai tsayawa a garin Damaturu na tsawon sa’oi biyu da safe.
Hakan ya sanya cibiyoyin kudi, kamfanonin gwamnati da mutanen da suka bude guraren cininkin su tashi da wuri saboda hatsaniyar.
Da farko rahotanni sun ruwai to cewa jami’an sojin Najeriya da soji sun fara bata-kashi da safen nan a kan wani dan rikicin da bai taka kara ya karya ba.
Ta bayyana cewa rikin ta fara ne a gidan hutun gwamnati misalin karfe 6 na safe zuwa karfe 10 na safe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here