Rundunar Sojan Nijeriya Ta Bada Tallafin Kayan Karatu Ga Makarantun ‘Yan Gudun Hijira A Adamawa

0
730

Muahammad Saleh, Daga Yola

RUNDUNAR sojan Najeriya ta bada kayan tallafin karatu ga makarantun ‘yan gudun hijira a sansanonin ‘yan gudun hijira a Adamawa.

Da ya ke gabatar da kayan tallafin karatun a madadin shugaban rundunar sojan kasar, shugaban rundunar soja ta 23 da ke Yola Birgediya Janar Benson Akinroluyo, ya bukaci a yi amfani da kayayyakin tallafin kamar yadda ya dace.

Ya ce yanzu lokaci ne da ya kamata a maida hankali wajan samar da ingantaccen ilimi ga yara ‘yan gudun hijira a sansanonin ‘yan gudun hijira daban daban a yankin arewa maso gabashin kasar.

“Akwai bukatar samar da ingantattun kayayyakin karatu ga yara ‘yan gudun hijira a sansanonin ‘yan gudun hijira a arewa maso gabas, rundunar soja za ta ci gaba da gudanar da ayyukan kwarai da zai kyautata rayuwar ‘yan Najeriya da ke sansanin ‘yan gudun hijira.

“Haka kuma malamai da muka samar duk jami’an sojoji ne da suke da kwarewar NAEC domin mu magance koke-koken gwamnatocin jihohi, kungiyoyi masu zaman kansu da hukumomi da suke ba da nasu gudumuwar fannin ilimi ga ‘yan gudun hijira”.

Da ya ke jawabi a taron shugaban hukumar ba da agajin gaggawa ta kasa NEMA reshen jihohin Adamawa da Taraba Alhaji Sa’ad Bello, ya yaba da matakin rundunar sojan kasar ya ce kai tsaye lamarin zai shafi rayuwar ‘yan gudun hijirar.

“Bisa irin wannan tallafi ga yara ‘yan gudun hijira ya taimaka wajen samun nasara a lokacin jarabawar yaran” inji Bello.

Ita ma dai da ta ke jawabi a taron kwamishiniyar ma’aikatar ilimi ta jihar Farfesa Kaletapwa Farauta, yaba wa kokarin rundunar sojan ta yi na bayar da kayan tallafin karatu ga ‘yan gudun hijiran, ta ce lamarin zai taimaka wajen samar wa yara ingantaccen karatu.

Ta ce a yanzu haka jami’an tsaron sojin sun samar da makarantu uku a jihar, ta kara da cewa gwamnatin jihar na maraba da wannan ci gaban kuma za’a kaddamar da makarantun da lamarin ya shafa.

Shi ma dai wakilin ‘yan gudun hijira da ke sansanin ‘yan gudun hijira na Malkohi Nicholas Samuel ya gode wa jami’an tsaron sojin da duk kungiyoyi dama hukumomin da ke aikin tallafawa ‘yan gudun hijiran.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here