Yadda Kamfanin Google Da Intanet Suke haifar Wa Jaridu Matsala……

  0
  1120

  Daga Mustapha Imrana Abdullahi

  GA dukkan masu karatun Jaridu musamman idan aka yi maganar irin shahararriyar kafar labarai ta Gaskiya Ta Fi Kwabo da aka fara wallafa wa a shekarar 1939 kuma aka yi amfani da ita wajen bayar da labarin yakin basasar Nijeriya sai kumar wadda ta zo daga bayanta New Nigeria idan ka cire Erohin Yoruba, za a iya cewa kafar yanar Gizo ko Intanet na haifar Wa da masu karatu da kamfanonin wallafa jaridu da kasidu gagarumin kalubalen da ya haifar Wa da kafafen labari ci baya musamman idan aka yi la\’akari da yanayin samun kudin shigar kamfanonin, rashin kudin shiga dai ya haifar wa  da kamfanonin da dama zama a cikin mawuyacin halin da ya sa \’yan bokon da suke aiki a wajen da sauran ma\’aikata kasancewa tamkar bayi.
  Ga Wanda bai san me ake cewa daukar hanyar ci gaba ba zai ce ta yaya a kasar da aka mayar ta  takardar shaidar kammala karatu da zama tamkar wata hanyar tsira daga Shan wahalar duniya? Kuma za \’a ce masu irin wadannan takardun za su zama bayi? To ga duk wanda ya sani sun zama bayi mana saboda sakamakon matsalar rashin kudin shiga ya sa kusan duk kamfanonin yada labarai a Nijeriya basa iya biyan ma\’aikata su misali wasu sun yi tsawon shekara daya, biyu ko shekara uku koma an kafa kamfanin kwata kwata babu wani tsarin biyan albashi Kuma ga masu takardun da ake maganar sun kammala karatu suna aiki a kamfanonin Ina maganar Ilimin ko satifiket?
  Hakan ya sa ake samun \’yan siyasa musamman ga wadanda suka fito fili suke yin amfani da takardun karya domin kawai su dare madafun iko wasu ma na kasashen waje suke yin amfani da shi musamman na makarantun da suka yi fice a duniya ko a Nijeriya indai za a bayar da masu gidan rana ga gungun wadanda ke aikin samo takardun jabun na karya da akwai mutane da yawa da ke wannan matsalar wasu Yan siyasa da ma aikata musamman na Gwamnati da suke da wannan matsalar domin da akwai wadanda suka ajiye aiki kafin ta tashi don kawai su karbi hakkokinsu wanda in sun bari ta tashi ba za su ga komai ba sai kora daga aiki.
  Wasu da a Nijeriya ake ganin su ne manyan kamfanonin jaridu tuni suka shahara wajen mikawa jama\’a takardar shaidar kai ma\’aikata su ne wato \”ID Card\” Amma a zahiri ba sa iya biyanka albashi ko kuma ba su taba biyanka albashi ba baki daya
  Kuma abin bakin Cikin hatta daikacin matakan Gwamnati uku sune suke dauka kafofin yada labarai su suke ba Talla da duk wata damar da ya dace Gwamnati ta taimakawa kamfani domin ya ci gaba, hasali ma ayyukansu sun Saba da irin tanajin aikin jarida domin sau da yawa aikin ya tsaya ne kawai a kan yin batanci da yada jita jita da labaru mara sa tushe balantana a kama su.
  Koda yake kamar yadda ake yadawa ne cewa ko su matakan Gwamnatin suna Yi da sune ba Don Allah ba ana dai Yi ne domin kada su rika tona ma katsamai asiri kan yadda ake kifa kwando ana ruf da ciki a kan dukiyar talakawan kasa.
  Kai akwai lokacin da wani ma\’aikacin da ke aiki da wata kafar yada labarai a matsayin Mai Kula masu da yankin arewacin Nijeriya yake Gaya mini cewa kamfaninsu na bin Gwamnatin Jonathan da ta shude bashin nera biliyan sama da biyu, Wanda shigowar wannan Gwamnati ta APC Mai tsantseni har ya haifar Wa kamfanin ya kasa biyan albashi na tsawon watanni domin Sai an tantance Kuma ga asusun ajiyar Gwamnati kwaya daya tak.
  Duk da Yan wadannan matsalolin da na lissafa domin ban Yi maganar kayan aiki irin na zamani ba, Sai ga batun yanar Gizo da yake Hana masu kokarin sayen Jaridu Don su fadaka ko sun gane.
  Sai kuma batun irin yawan kwafin Jaridu da kamfanonin ka iya Wallafa wa a duk rana domin zakaga kamfanin jarida yana gari kamar Legas Amma Sai ya rika kawo a kalla kwafin jarida arba\’in Hamsin ya yi yawa dubu daya ko biyu a Jihar da ke da yawan jama\’a a tarayyar Nijeriya da suka Kai sama da miliyan Sha biyar ko Mai mutane miliyan shida ko bakwai amma fa ga kamfanin na karbar tallace tallacen jama\’a a kan kudi masu yawa na akalla shafi Mai kala yana kamawa dubu Dari biyar da wani abu har zuwa Dari bakwai Kuma duk hakan na faruwa ne ba tare da masu bayar da tallar sun San irin yawan jaridun da ake kaiwa jihohin ba domin amfanin bada Talla shi ne a samu jama\’a da yawa su samu sakon da ka aika zuwa gare su.
  Da wannan ne ma wasu masana me cewa ana yin asarar kudi kawai ba tare da an San abin da ake yi ba na rashin zagayawar kwafin jaridun da ake bugawa, da wannan ne wasu ke cewa shin ana Cin Amanar Masu bayar da tallar?.
  Wani al\’amari Kuma shi ne na kamfanonin da ke karbar tallace tallacen suna bayarwa ga kafafen yada labarai Suma saboda matsuwar da suka yi na su karbi Talla basa tsayawa su Gaya wa Wanda zai ba su tallar gaskiyar da ya kamata Kodayake Suma basa kokarin biyan kafofin da ke Yi masu tallar a kan Kari domin a wasu lokutan Sai an Kai ruwa rana.
  Sai kuma irin rawar da kafofin yada nau\’o\’in labarai daban daban kama daga hoton da ke bayar da labaru, bidiyo da rubutaccen labari ko sharhi ke takawa musamman a wannan zamani na yanar Gizo ko Intanet domin ya yaka rawa wajen haifar da matsaloli da dama duk da cewa a bangare daya Kuma ya saukaka abubuwa.
  A Mafi yawan lokaci zakaga kafar kafar manhajar matambayi baya baya\”Amma idan Yan jarida da masu rubutu sun rubuta\” yake samun manya manyan kamfanonin da suke bayar da tallace tallacen suna ba kafar Google\” Talla Sai su Kuma su rika ba kamfanonin yada labarai da sauran shafukan yanar Gizo Talla Wanda hakan na haifar Wa jaridun gargajiya nakasu domin abin da matambayi baya bata idan wani ko wasu sun yi rubuce rubuce ko hotuna da bidiyo yake kamawa ya ajiye yake biyan kafofin sadarwa abin bai taka Kara ya karya ba.
  Kuma lamarin Intanet ya haifar Wa kafafen labarai na Nijeriya da sauran duniyar labarai gagarumar matsalar da ke neman ta gagari kundila ta fannoni da dama.
  Kamar yadda wani Mai sana\’ar sayar da jaridu da Mujallun Nijeriya da ya shafe shekaru 25 yana wannan sana\’ar Amma yanzu ya koma harkar sayar da burodi ya shaida mini cewa lallai babu shakka yanar Gizo ta haifar Wa Jaridu matsalar da in ba a Yi sannu ba Sai labari kawai Nan gaba.
  \”Wannan sayar da burodin yafi jarida domin a yanzu abin da zan samu ba zan same shi a tallar jarida ba duk da yawan shekarun da na Yi Ina Yi, wannan burodin ban Kai ko wata biyu ba Amma yafi tallar jarida, jarida fa Sai ka Kai ga sayar da kwaya 30 sannan ka samu dubu daya Kuma a yanzu Ina Gaya Maka da wahalar gaske ka samu wani da ke yawon sayar da jarida a cikin gari da zai wuce sayar da kwafi Goma Sai idan a babban titin shigowa babban birni yake tallar, Don haka ta Yaya za a hada su\”inji Mai sayar da burodi.
  Shi dai wannan Mai burodi ya ci gaba da cewa akwai lokacin da kamfanonin Wallafa Jaridu Na arewacin Nijeriya a wasu shekaru can baya suka Tara wani taro a otal suka gayyace mu bayan kowa ya kammala bayanansa Sai na tashi na ce masu.
  \”Kodayake mu ba Yan boko bane mun tsaya ne a gargari, Amma  ku kuna Yi mana kallon jakuna mu Kuma masu sayar da jaridun Muna Yi maku kallon Awaki, Sai aka yi dariya nace abin da za ku Yi shi ne kada ku rika saurin Wallafa labarai a yanar Gizo Sai bayan Sha biyun rana domin masu sayen jarida su saya kada a ci gaba da samun kwantai, to ga shi magana ta bayan Yan shekaru itace ta tabbata kowane kamfanin buga Jaridu ya shiga wahalar rashin cinikin da in ba sa a ba Nan gaba kadan Sai dai a rufe shago\”.
  Bincike ya nuna tuni dai wadansu kamfanonin Wallafa Jaridu suka koma idan za su yi aikin Sai dai kawai a Wallafa iya wadda ake jin za a Yi amfanin da ita, ga shi kusan kullum kayan aikin Kara tsada suke Yi da yasa ba a samun karuwar kamfanonin Sai raguwa duk da matsalar rashin dagewa ayi karatun labarai da kasidu musamman a yankin arewa.
  Kodayaushe za a samu warware wadannan matsalolin da ke Yi wa sana\’ar jarida barazana?

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here