CUTAR SANKARAU NA CI GABA DA YIN MUMMUNAR TA\’ASA A JIHOHIN AREWA

0
774
Daga Usman Nasidi
AKALLA mutane 33 ne suka rasa rayukansu a Jihar Naija bayan sun kamu da cutar sanƙarau, a cikin mutane 116 da aka kiyasta sun kamu da cutar
Shugaban hukumar kula da lafiya a matakin farko ta jihar, Yahaya Na\’uzo ya bayyana haka inda ya ce mutane 9 sun mutu ne sanadiyyar kamuwa da cutar nau’in Type C, yayin da ragowar mutane 24 suka mutu sanadiyyar kamuwa da ƙwayar cutar nau’in A da B tun lokacin da annobar cutar ta ɓalle a jihar.
A cewarsa, rahotanni na bayyana cewa an samu nasarar killace cutar a ƙananan hukomimin Rijau, Kontagora,Magama da Agwara.
Ya ce rahoton ɓullar cutar da aka samu a ƙananan hukumomin Paiko da Suleja, mutanen da aka samu da cutar matafiya ne.
Ya yi ƙarin bayanin cewa tun bayan samun mutuwar mutun na farko sanadiyyar cutar, gwamnati jihar ta shiga wayar da kan jama’a a kan matakan kariya daga cutar.
Ya ce: “Yanzu muna samun ƙarancin rahoton ɓullar cutar saboda an faɗakar da al’ummomi kan su kai rahoto asibiti mafi kusa da zarar sun ga mara lafiya na nuna alamun cutar.
“An ilimantar da mutane kan su kai rahoto asibiti mafi kusa da zarar sun ga alamun zazzaɓi, amai da kuma riƙewar wuya.”
Ya shawarci mutane da su guji ɗabi’ar magani da kansu, sannan su kai kan su asibiti da zarar sun ga alamun cutar.
Na’uzo ya kuma shawarci mutane da su riƙa buɗe ƙofofi da kuma tagogi don samun wadatacciyar iska a ɗakunansu. Sannan kuma su riƙa wanke hannunsu a kodayaushe.
A karshe ya ƙara da cewa an tura jami’an lafiya zuwa yankunan karkara don ganin an ɗakile yaɗuwar cutar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here