Kisan Gillar Sheikh Jafar: Shekarau Na Kano Da Goje Na Gombe Suna Da Hannu?

1
1467

Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna

A kokarin ganin an yi wa kowa adalci ta hanyar ajiye kowone abu a muhallinsa, Rundunar \’Yan Sandan Tarayyar Nijeriya sun bayyana samun wadansu takardun bayanai na sirri da suke alakanta tsohon Gwamnan Kano Ibrahim Shekarau da kisan babban malami Sheikh Jafar Mahmood Adam Kano.
Idan dai za a iya tunawa an kashe Jafar Adam ne lokacin da yake jagorantar sallar asuba a gidansa da ke unguwar Dorayi a Kano babban birnin jihar.
Shi dai samamen da rundunar \’yan sandan ta kai, samemen bincike ne a gidan tsohon Gwamnan Jihar Gombe Danjuma Goje, Kuma a nan ne ta yi katarin ganin wadannan takardun sirri da suke bayanin yadda aka shirya yin kisan.
\’Yan sandan sun kuma gano tsabar kudi makudai a gidan da suka kai miliyan 18 na takardun Naira, sai kuma takardun kudin Riyal na kasar Saudiyya dubu sha tara, duk a cikin gidan Goje na Gombe, wanda Sanata ne a halin yanzu.
Kamar dai yadda aka sani a shekarar 2006 ne wadansu \’yan bindiga suka dira cikin gidan marigayi Sheikh Jafar Adam cikin masallacinsa da ke unguwar Dorayi suka bude masa wuta, wanda hakan ya yi sanadiyyar rasa ransa baki daya.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here