An Cafke Mutum 39 Masu Miyagun Laifuffuka A Kuros Riba

0
817

MUSA MUHAMMAD KUTAMA Daga  Kalaba

RUNDUNAR ‘yan sandan Jihar Kuros Riba ta ce ta yi katarin cafke wasu masu laifuka da suka addabi babban birnin jihar Kalaba  da kuma sauran sassan jiha da fashi da makami , kana kuma da kama mutane ana garkuwa da su da kuma fadace-fadace na matasa  ,yan  kungiyar asiri da adadin yawan wadanda aka kama  su ya kai  mutane talatin da tara.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Hafiz Muhammad Inuwa ,ne ya sanar da haka ga manema labarai a ofishinsa.Ya ce daga cikin barayin da aka kama har ma da wadanda suka kware wajen satar motoci cikin wadanda aka kama akwai Ibrahim Musa, Denis Ogbeche ,da aka kama su da wata mota da aka sato a Itu jihar Akwa Ibom suka yi hadari da ita a kauyen Ikanda yankin Karamar hukumar Bekwarra babbar hanyar da ta hada Vandekya Jihar Benuwai da Kuros Riba .Bangaren fashi da makami har wayau Hafiz Inuwa kwamishinan ‘yan sandan ya ci gaba da cewa wani mutum mai suna Charles Hillary ya kawo rahoton a karamin ofishin ‘yansanda na rukunin A cewa gungun wasu matasa da yawan su yakai su 6. Suka kai masa hari a gidansa suka kwace motarsa da kudi Naira 150.da wayar sa ta  tafi da gidanka .

Ya ci gaba da cewa su kuma masu fadan kungiyoyin  asiri da suka hana mutanen birnin Kalaba mike kafafuwansu su huta a gidajen su da sauran sassan gari an kama mutum hudu daga cikin su Edward Agbor,Etta Obibia, da Fred Ntana sannan kuma Sunday Usang. Da  ya juya kan wadanda ake zargi da laifin kama mutane ana garkuwa da su kwamishinan ‘yan sandan ya ci gaba da cewa an kama Jacson Out da Basil Olom da ake zargi da kitsa kama Victor Uchenna Okike, da ke garin Ogoja, an kuma same su da miyagun makamai da suka hada da adda,wayoyin tafi da gidanka da kuma wayar salula kirar Nokia da harsasai da kuma kayan ‘yan sanda tare da wata mota kirar Toyota mallakar wani mutum mai suna Etete Cardiff Offiong Olom da ma yana daya daga cikin wanda rundunar ‘yanda ta baza komar kama shi bisa zargin hada baki a kama Maciej Taszek, dan kasar Poland wanda har yanzu maganar ma na gaban kotu a nan Kalaba.

Kwamishina  Hafiz Muhammad Inuwa na kusa da kammala yi wa manema labarin irin nasarorin da suka samu da kuma kokarin da sukayi sai ga labarin kama wasu mutum goma sha uku ‘yan kungiyar asiri ya kutso kai ofishin nasa,  ‘yan kungiyar asiri da suke fada da juna tsakanin kungiyar Vikings da kungiyar K.K.K. A karamar hukumar Akamkpa dukan su matasa ne da ko shekara talatin ma ba su kai ba ragowar abokan tsagerancin nasu ciki har ma da wata budurwa mai suna Nkoyo Bassey Martins Oyama . Shi kuma an same shi da kayan tsubbu na al’adunsu.Bincike halin yanzu na ci gaba da gudana da zarar an kammala kuma kotu za a mika su inji kwamishinan.

 

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here