MA\’AIKATA SUN YI WA SARAKI, DOGARA DA MINISTA IHU YAYIN BIKIN RANAR MA\’AIKATA

0
806
Daga Usman Nasidi
\’Ya\’yan kungiyar kwadago ta kasa, NLC sun yi ma shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki da Kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara da kuma ministan kwadago ihu tare da kiran su barayi yayin gangamin taron ma’aikatan a yau Litinin 1 ga watan Mayu.
Ma’aikatan sun rikita filin gangamin ne kan bukatarsu na lallai sai gwamnati ta fara biyan su karancin albashi na N56,000, kamar yadda jaridar Sahara Reporters ta ruwaito.
Lamarin ya yi kamari ne daidai lokacin da aka kira wakilin ministan kwadago, babban sakatare a ma’aikatan kwadago Abiola Bawa da ya fito don ya yi jawabi a madadin minista a filin taro na Eagle Square.
Wannan sai ya harzuka ma’aikatan da suke ganin ministan bai mutunta su ba da ya aiko wani ya wakilce shi bayan shi kansa ya kamata ya wakilci shugaban kasa Muhammadu Buhari ne.
Wata majiya ta bayyana mana daga nan suka fara ihu ‘ba ma yi, ba ma yi, ba ma yi’, ‘Barawo, barawo, barawo!’ ‘A biya mu karancin albashi! A biya mu karancin albashi!’
Hakan yayi matukar bata ma ministan rai, inda ya fasa gabatar da jawabin, ya koma kujerarsa ya zauna. Daga nan sai shuwgabannin NLC suka kira tsohon shugaban kungiyar Adams Oshiomole don ya kwantar da hankalin ma’aikatan, amma ma’aikatan suka ci gaba da yi masa ihu.
Daga nan sai ma’aikatan suka matsa zuwa inda manyan baki ke zama, hakan ya sanya \’yan sanda korarsu, inda su kuma manyan bakin suka ruga daga wajen.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here