Dokar Kwaji Kafin Aure: Majalisar Dokokin Jihar Adamawa Ta Saurari Ra’ayoyin Jama’a

0
673

 Muhammad Saleh, Daga Yola

MAJALISAR dokokin Jihar Adamawa ta saurari ra’ayoyin jama’a game da yunkurin kafa dokar gwajin jini domin tantance kwayar cutar HIV kafin daurin aure.

Da yake magana a lokacin sauraren ra’ayoyin jama’ar, Kakakin majalisar dokokin jihar Kabiru Mijinyawa, ya ce duk wani abu da ya kamata a yi domin shawo kan yaduwar cutar HIV/AIDS za a yi domin shawo kan cutar a cikin al\’umma.          

To sai dai ita kuwa shugabar kungiyar masu dauke da kwayar cutar HIV ta jihar Misis Farah James ta nuna fargabar samun karuwar mace-macen masu dauke da cutar idan kungiyoyin kasa-da-kasa da kungiyoyi masu zaman kansu suka janye tallafi da suke bayarwa.

Ta ci gaba da cewa tado da batun kafa dokar gwaji kafin auren za ta haifar da karuwar masu bukatar maganin da dama, maganin ya’yi karanci a daidai lokacin da kungiyoyin ke kokarin janye tallafin da suke badawa.

Haka shi ma babban sakataren cibiyar kula da masu dauke da kwayar cutar HIV ta jihar Dokta Stephen John, ya yi wa kwamitin majalisar dokokin kan sha’anin lafiya bayanin cewa an sami karuwar ma su dauke da cutar HIV a jihar, ya danganta lamarin da ayyukan ‘yan ta’addan kungiyar boko-haram.

To sai dai da take maida kalami kan wannan batu kwamishiniyar ma’aikatar lafiya ta jihar Dokta Fatima Atiku Abubakar,  ta ce janye tallafin kungiyoyin kasa-da-kasa ba zai  zama barazana ga kokarin yaki da cutar ba, saboda akwai tsarin da gwamnatin tarayya da jihohi suka bullo da shi.

Ta ce gwamnatocin na cire wani kaso daga kudin haraji da ma na shiga daga asusun gwamnatin tarayya don sayen magunguna kai-tsaye domin kauce wa karkatar da kudaden idan aka bayar hannun gwamnatocin jihohin a kasar.

Kakakin majalisar dokokin jihar Kabiru Mijinyawa, ya ce idan dokar ta sami amincewar majalisar dokokin da ta zartaswa za a hukunta wanda ya taka dokar  hukunci mai tsanani, musamman idan daya daga ciki cewa yana da cutar HIV amma ya boye, ya ce za a hana daurin auren kwata-kwata idan ba a yi gwajin ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here