\’YAN MAJALISA SUN NUNA SON ZUCIYA KAN KARA WA KANSU KUDADE A KASAFIN KUDI-ISMA\’ILA BELLO

  0
  707
  Isah Ahmed, Jos
  WANI malamin a sashin nazarin tattalin arziki da ci gaban kasa na jami\’ar jihar Bauchi Malam Isma\’ila Bello Usman,  ya bayyana cewa abin da \’yan majalisar kasa  suka yi na kara wa kansu kudade a wannan kasafin kudi  na shekara ta 2017 da suka sanya wa hannu a makon da ya gabata, son zuciya ne.
  Malam Isma\’ila Bello Usman ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu.
  Ya ce a  cikin wadannan \’yan majalisa akwai  tsofaffin gwamnoni da tsofaffin janar janar na soja tsofaffin da  manyan ma\’aikata da sauran manyan masu kudi, wadanda sun mallaki komai na rayuwa. Ya ce ya kamata su tausayawa al\’ummar Nijeriya  kan mawuyacin halin da suke ciki, maimakon kara wa kansu kudade a wannan kasafin kudi.
  Malam Isma\’ila Bello ya yi bayanin cewa a wannan  kasafin kudi akwai bangarorin da suka shafi ilmi da kiwon lafiya da aikin noma da  ya kamata a ce \’yan majalisar,  nan sun kara kason da aka warewa wadannan bangarori saboda mahimmancinsu. Amma \’yan majalisar nan ba su yi haka ba.
  Ya ce idan aka dubi wannan kasafin kudi, ba zai yi wani  tasari ba, wajen bunkasa tattalin arzikin kasar nan, domin kudaden da aka ware don  biyan  ma\’aikata kudaden albashi da alawus alawus  sun fi kudaden da aka ware don gudanar da manyan ayyuka.
  \’\’Har yanzu talakawan Nijeriya suna  shan wahala, kuma har yanzu talakawan Nijeriya suna  tare da wannan gwamnati saboda sun yi imani cewa ita ce za ta magance masu matsalolin da suke ciki. Amma talakawan Nijeriya suna ganin cigaba da matsalolin da suke ciki suna  tasowa  ne sakamakon takun sakar da ke tsakanin shugaban kasa da \’yan majalisun kasa. Saboda haka ya kamata \’yan majalisun  su canza halayensu domin gwamnati ta sami damar aiwatar da kudurorin da ta sanya a gaba\’\’.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here