Kwamishinan ‘Yan Sanda Ya Ja Kunnen Hausawa

0
804

MUSA MUHAMMAD KUTAMA, Daga Kalaba

KWAMISHINAN ‘yan sandan Jihar Kuros Riba, Hafiz Muhammad Inuwa ya gargadi iyaye da yaran Hausawan Unguwar Hausawa ta Layin Bagobiri da su rika tsawatarwa ‘ya’yansu ko kuma su kuka da kan su.Kwamishinan ya nuna bacin ransa game da yadda Layin Bagobiri Unguwar Hausawan barayi suka mayar da ita babbar kasuwarsu da suke sayar da kayan sata idan sun sato kuma  ta yi kaurin suna waje saye da kuma sayar da kayan sata.

Ko a kwanan baya unguwar ta baci da sunan satar baturan manyan motoci masu dakon kaya daga Kurmi zuwa sassan kasa ko kuma suka dauko daga wasu wurare na Arewa suka kawo Kalaba idan sun ajiye motocin su a unguwar kafin gari ya waye sai direba ya iske da safe an sace masa baturan mota lamarin da shugabannin kungiyar daya daga cikin su Alhaji Auwalu Yahudu ya koka a madadin kungiyar.direbobin manyan motocin .

Da yake yi wa wakilinmu na kudanci karin haske game da sakon shugaban ‘yan sanda Kuros Riba Alhaji Salisu Abba Lawal Sarkin Hausawan Kalaba  ya ce “wani uzuri ne ya kai Alhaji Usman mai magana da yawun al,ummar Hausawa wurin kwamish nan aka yi dace da akwai wasu yara daga nan Bagobiri da ake zargin su da sayen wayoyin hannu na sata suke tsare a ofishin ,yan sanda ganin haka ya sanya ya aiko shi ya ce a gaya wa iyaye su ja wa ‘ya’yansu kunne su kuma masu sayen kayan sata su daina domin duk wanda aka kara kamawa da sunan sayen kayan sata zai dandana kudarsa”.inji Sarkin Hausawan.

Karshe kwamishinan ya jadda wa ‘yan arewar cewa  su shiga taitayin su domin duk wanda ya shigo hannu da sunan mugun hali zai yaba wa aya zaki.A kokarin da ya yi na isar da sakon kwamishinan ‘yan sandan ga al,ummarsa Alhaji Salisu Abba Lawal ya tatttara masu sana’ar cajin batirin waya da kuma saye da sayar da kayan waya ya isar masu da sako in ya so idan kunne ya ji  jiki ya tsira.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here