Sun Dakatar Da Binciken Sarkin Kano Sanusi Lamido

0
696

Daga Zubairu Abdullahi Sada

MAJALISAR dokokin Jihar Kano ta dakatar da binciken da take yi wa mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi Lamido II kan wasu batutuwa da suka shafi almubazzaranci da dukiya da wasu gwalangwalantu da shi Sarkin yake famar aikatawa.

Majalisar ta yanke dakatar da binciken ne bayan da ta karbi wata wasika daga Gwamnan jihar Dokta Abdullahi Ganduje wadda shugaban majalisar Honorabul Kabiru Alhassan Rirum ya karanta wa mambobinsa a zauren majalisar.

Abin da wasikar Gwamna Ganduje ta kunsa cewa ta yi, \’\’ina kira da ku sargafe wannan bincike sakamakon shiga tsakani da wasu manyan kasa suka yi kan wannan batu\’\’.

Wadannan manyan kasa kamar yadda wasikar ta bayyana sun hada da Mukaddashin shugaban kasa, Yemi Osinbajo da shugabannin jam\’iyya da tsofaffin shugabannin kasa, wato Ibrahim Badamasi Babangida da Abdulsalami Abubakar da mai martaba Sultan na Sakkwato, Sa\’ad Abubakar da \’yan kasuwa na jihar, Aliko Dangote da Aminu Dantata.

Gwamna Ganduje ya ce, duk da ba ya shiga sha\’anin ayyukan \’yan majalisar, to, yana rokon su da su duba al\’amarin da idon rahama su janye binciken domin zaman lafiya ya dauwama. Ya ce, \’\’ Tun da ni ina ba ku matsayinku na wani bangare na gwamnati, kuma kuna da \’yanci da damar binciken Sarkin, ina rokonku ku janye tare da dakatar da binciken don a sami zaman lafiya mai dorewa\’\’.

Ya ce, an yi taro a Kaduna a kan wannan batun a gaban wasu Gwamnoni, Sarkin Kano Sanusi Lamido shi da kansa ya amsa laifukansa da kurakurensa kuma ya yi alkawari zai gyara, to, a ganinsa dalilin hakan ya kamata su duba al\’amarin da idon rahama.

\’Yan majalisar dokokin Jihar Kano din dai tuni suka tattauna wannan batu tare da amincewa su janye dakatar da binciken Sarkin Kanon dalilin rokon nasu da aka yi kan hakan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here