Sun Sayar Da Diyarsu Naira Dubu 400 Domin Biyan Haya

0
716

MUSA MUHAMMAD KUTAMA, Daga Kalaba

‘YAN sanda a Jihar Kuros Riba ta sanar wa manema labarai kama miji da mata  Sunday Udoh da matarsa mai suna Victoria a garin Ikom saboda zargin sayar da ‘yar su kan kudi Naira Dubu 400 .Da yake gabatar wa manema labarai wadanda ake zargin aka kama su kwamishinan ‘yan sandan jihar, Hafiz Muhammad Inuwa ya ce sun shiga hannu ne ta hanyar kyankyasa wa rundunar da aka yi ne.

Haka nan kuma a bayanin da kwamishinan ya yi wa ‘yan jaridar ya ce bisa bayanai da suka yi wa jami’an su na dalilan da suka sanya su yanke hukuncin sayar da ‘yar tasu mai shekara 6 da haihuwa shi ne za su biya kudin hayar gidan da suke haya kana kuma su bude kasuwanci da ragowar kudin.

Kwanan baya ne rundunar ‘yan sanda da ke ofishin Ikom suka samu labari nan take suka garzaya cikin aikin nasu suka yi katarin kama wadanda ake zargin .Sai dai kuma Sunday Udoh uban yarinyar ya karyata zargin sayar da ‘yar tasa ya ce hakika al’amura sun yi mana tsauri ba gaba ba baya ni da matar tawa amma ba mu sayar da ‘yarmu ba don mu fita daga talauci ba .”inji shi.

Yanzu haka dai an kawo wadanda ake zargi sashen binciken masu aikata miyagun halaye na hedkwatar  rundunar ‘yan sandan da ke Kalaba kuma da zarar  an gama binciken su kotu za,a mika su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here