TA KASHE KAN TA DA KWANKWADI GUBA KAN SABANIN DA TA SAMU DA MIJINTA

0
691
Daga Usman Nasidi
WATA mata mai suna Halima Kabiru ta kashe kanta ta hanyar kwankwadar guba a sakamakon sabani da ta samu da mijinta.
Ma’auratan wadanda ke zaune a unguwar Afita Mama Pandogari, da ke mazabar Kagara a Jahar Neja sun yi fada ne a kan ruwan sha, kamar yadda mijin matar mai suna Musa Kabiru ya bayyana wa ‘yan sanda.
Kabiru ya ce jim kadan bayan sun yi fadan ne sai ta sha guba ta suma, lamarin da ya sa aka garzaya da ita asibiti inda ta rasu.
Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar , Bala Elkana ya ce sun samu labarin abun ne daga bakin mijin, wanda ya kira su a lokacin da matar ta kwankwadi gubar. Ya ce suna kan bincike game da al’amarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here