KOTU TA DAKATAR DA GWAMNA EL-RUFA\’I DAGA RUSHE KASUWAR BARCI

0
770
Daga Usman Nasidi
BABBAR kotun Jihar Kaduna ta dakatar da gwamnatin jihar daga rusa fitacciyar kasuwar nan da ke cikin garin Kaduna, kasuwar barci, har sai ta kammala sauraron karar da \’yan kasuwar barci suka shigar.
Alkalin kotun mai shari’a Mohammed Bello ya umarci dukkanin bangarorin da su saurara ga daukan kowanne irin mataki har sai kotu ta gama sauraren karar, kamar yadda jaridar GTK ta ruwaito.
Majiyarmu ta bayyana cewa wasu mutane goma sha shidda ne suka shigar da gwamnatin Jihar Kaduna da hukumar kasuwannin jihar ta Kaduna kara a madadin \’yan kasuwar barci don a hana su rusa kasuwar.
Wadanda suka kai karar sun hada da Auwalu Hussain, Kabiru Usman, Aminu Ahmed, Bawa Ahmed, Josia Sunday, Ndubueze Egbo-Ogu, Augustine Sunday, Ali Abdulhamid, Maryam Abubakar, Rabi\’atu Musa, Latifah Yusuf, Amina Abdulrauf, Aishatu Ibrahim, Hafsat Uba, Sa’adiya Ahmed da Wasilat Ahmed.
Lauyan masu kara Mista Elisha Kurah, SAN ya bukaci kotu da ta dakatar da rushe kasuwar, sa’annan ya roki kotu da ta bayyana idan gwamnati na da ikon rushe kasuwar . Sa’annan lauyan ya danganta bukatarsa ga sashi na 7(1) da (5) na kundin tsarin mulkin kasa.
Lauya Kura ya nemi kotu ta tabbatar da idan Gwamnan jihar na da damar sallamar \’yan kasuwan ko a’a, daga karshe lauyan ya bukaci kotu ta hana Gwamnan jihar rusa kasuwar, sa’annan kuma kotu ta yanke hukuncin cewa gwamnatin jihar ba ta da ikon kwace kasuwar daga hannun karamar hukuma zuwa ga \’yan kasuwa.
Bugu da kari, lauyan ya bukaci kotu ta yanke hukuncin cewa gwamnatin karamar hukuma ke da damar kula da kasuwannin jihar, musamman Jihar Kaduna, don haka lauyan ya kara neman wata bukata daga kotu da ta bayyana barazanar rushe kasuwar da gwamnatin jihar ta yi wa kasuwan a matsayin karan tsaye.
Daga karshe Alkali Mohammed Bello ya dage sauraron karar zuwa ranar 5 ga watan Yuni.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here