Kwadayin Naira 200 Ya Kai Ni Sato Yarinya – Nwanne

0
808

MUSA MUHAMMAD KUTAMA, Daga Kalaba

WATA budurwa mai suna Nwanne wadda yanzu haka na tsare a ofishin ‘yan sandan jihar Abiya sakamakon furtawa da ta yi da bakinta ba kuma tilasta mata aka yi ba cewa Naira 200 wata mace mai suna Chinemerem Isiah, ta  bata ita kuma ta sato mata wata yarinya ‘yar shekara 3  da haihuwa a wani gida a kauyen Alaoji.

Yadda har hakan ta kasance kamar yadda Gaskiyatafikwabo  ta samu labari  yarinya Nwanne ta ce ta hadu da Chinmemerem ne a hanya lokacin kkuma babanta ya aike ta daga nan ita kuma sai ta kirawo ta ta bata kudi naira metan ta ce ta je ta daukomata yarinya a wani gida tayi sa,ar hakan kuma ta kawo mata ita domin a cewar wadda ta aike tan yar tace taje ta dauko mata ita kafin daga bisani kuma cibi ya kasance kari.

Ko yaya aka yi ma har ita yar aiken ta yi katarin iya raba yarinyar da gidansu Nwanne ta ce “nuna masu kudin na yi na ce su zo mu je in saya masu alawa da biskit har yarinya daya ta biyo ni sai kuma ta ki sai wannan ce da aka kama mu da ita ta amince ta biyo ni ni kuma na kai wa matar da ta tura ni”.inji ta.

Adeleye Oyebade shi ne kwamishinann ‘yan sandan jihar Abiya wanda ya gabatar da masu laifin da ake zargi ga manema labarai yace mahaifiyar yarinyar da aka sace ce mai suna Rose Ndukwu ce ta sanarwa da ofishin yan sanda da ke Ogbon Hill garin Aba,cewa ‘yarsu ta bata ba a san wanda ya dauke ta ba daga nan su kuma suka baza komar su har sukayi sa,ar cafke su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here