OGOMO PENGANA YA BUKACI A SANYA SOJOJI A HANYAR JINGIR ZUWA JOS

0
841
Isah  Ahmed, Jos
MAI martaba Ogomo Pengana Esua Mamman Shayang  da ke karamar hukumar Bassa a Jihar Filato ya yi kira ga gwamnatin Jihar Filato da sauran hukumomin tsaron jihar,  su sanya wuraren binciken sojoji  a dajin nan na kan hanyar garin Jingir zuwa Jos don magance matsalar yawan fashi da makami da ake yi a wannan daji. Ogomo Pengana ya yi wannan kira ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a fadarsa da ke garin Jingir.
Ya ce baya ga yawan fashin da ake yi a wannan daji a kusan kullum. Fashi da makami ya zama kamar ruwan dare a yankin masarautar  Pengana.
Ya ce kusan a  kullum dare da rana sai \’yan fashi da makami sun tsare kan hanyar nan ta Jos zuwa Jingir sun yi wa matafiya fashi, sun kashe mutane sun kwace masu kudade. Bayan haka \’yan fashin suna bin gida-gida a garuruwan wannan yanki, suna yi wa jama\’a fashi da makami.
\’\’A yanzu mutane suna cikin tashin hankali a wannan yanki sakamakon wannan yawan fashi da makami da ake yi. Don haka muna rokon gwamnati ta kawo mana sojoji a wannan  daji na Jingir, su zauna don magance wannan matsala. Kuma a dawo da sojojin da suke garin Fuskar Mata da aka cire. Domin tun da aka cire wadannan sojoji aka shiga cikin zulunmi a wannan gari. Kuma a sanya mana motocin sojoji da zasu rika yin sintiri kan wannan hanya, domin magance wadannan \’yan fashi da suka addabemu a wannan masarauta\’\’.
Ogomo Pengana ya yi kira ga gwamnatin jihar ta gyara siton ajiyar taki na garin Jingir da iska ta kwashe a kwanakin baya. Ya ce sakamakon lalacewar wannan sito a bana ba a kawo  taki ba, duk da gwamnati ta kai taki wurare da dama a wannan karamar hukuma. Don haka muna rokon gwamnati ta taimaka ta gyara mana wannan sito na ajiye taki
da ya lalace.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here