Ta Aika Mijinta Lahira Saboda Kallon Fim

0
812
 Mustapha Imrana Abdullahi
A wani al\’amarin da ke da matukar daure kai wata mata mai suna Aisha Idris, ta kashe mijinta, mai suna, Muhammed Auwal Ladan, ta hanyar watsa masa tafasasshen ruwan Zafi, saboda ya hana ta kallon Fim, din Ali-Nuhu, inda ya ce ta tashi ta yi sallah, abin da ya jawo sanadiyyar rasa ransa.
Lamarin wanda ya faru ne a Unguwar Jahun da ke Jihar Bauci, a Larabar makwan da ya gabata, ya ba wa al’ummar unguwar da dama mamaki da ban al’ajabi.
A bayanan da aka samu daga jama\’a suna tambayar cewa shin me ya sa wasu mutane ke aiwatar da irin wannan aikin na kisan kai domin tsananin kallon fina-finai kawai, Allah ka ci gaba da yi mana tsari da irin wannan hauka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here