Ya Kona Budurwarsa Kan Ta Ki Ta Haihu Da Shi

0
841

MUSA MUHAMMAD KUTAMA, Daga Kalaba

WANI matashi mai suna David a garin Fatakwal Jihar Ribas ya shiga hannun ‘yan sanda sakamakon zarginsa da ake yi na kona budurwarsa  Uchechi Okorie da kananzir domin ta ki yarda ta haihu da shi kamar yadda wannan jarida ta samu labari.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda ta Jihar Ribas, Nnamdi Omoni ya tabbatar wa Wakilinmu na Kudanci haka ya ce “tabbas David ya juye galan din man kananzir a jikin budurwar mai suna Uchechi  Okorie,sannna bayan ya jiketa da shi ya kunna mata wuta. Jami’in ya ce budurwar ba karamin konewa ta yi ba lamarin da ya yi muni ba a ma ko iya gane fuskarta da ma wasu sassan jikinta.inji shi.

Haka nan kuma rundunar har wa yau ta bayar da labarin wasu da suka kware wajen damfara ta yanar gizo su biyu Stephen Ikatubo da Micheal Basil bayan sun yi katarin cire wasu makudan kudi a bankin kasuwanci na New Generation da ke birnin Fatakwal.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here