BAN JI DADIN YADDA PANTAMI YA YI MANI TAYIN SHIGA MUSULUNCI BA – Inji Minista Dalung

3
1054
Daga Usman Nasidi
MINISTAN harkokin matasa da wasanni Solomon Dalung, ya soki lamirin hanyar da Sheikh Isa Ali Pantami ya bi wajen kiransa da ya shiga addinin Musulunci, kamar yadda ya sanar a shafinsa na Facebook.
A makon da ya gabata ne dai NAIJ.com ta ruwaito muku ministan ya kai ziyara a Masallacin Annur da ke Abuja inda Sheikh Pantami ke gabatar da Tafsir cikin watan azumi.
Dalung ya ce ya saurari ra’ayoyin jama’a da dama dangane da ziyarar tasa, amma ya ce a gaskiya Shehin malamin ya tozarta shi ta yadda ya gayyace ya shiga Musulunci,inda ya ce:
“Tayin da Pantami ya yi mini ba da zuciya daya ya yi shi ba, kuma ba a kan tsarin Musulunci ba ne. Da farko dai ba shi ya gayyace ni Tafseer din ba, da kaina na je\’\’.
“Na yi mamakin yadda Pantami ya ki yin koyi da Annabi SAW, wanda da ya karbi bakoncin tawagar Kiristoci daga birnin Sinai, kuma ya karbe su hannu biyu-biyu ba tare da ya yi musu tallar Musulunci ba, asali ma kyale su ya yi suka yi bautarsu a masallacin.”
Dalung ya ci gaba da fadin cewa kimanin shekaru biyar kenan yana zuwa tafsir a masallatai daban-daban, domin karfafa dangantaka tsakanin addinin Kirista da na Musulunci, kuma ba a taba yi masa haka ba,
“Pantami ya yi amfani da damar ne don kawai ya bata mini suna, Idan da a ce da gaske yake, me ya sa tun can baya bai taba yi mini kiran ba, sai da na ziyarce shi? Ko kuma ya aiko mini a rubuce ba? Ina mu’amala da manyan Musulmai da dama kamar su Sheikh Lemu, Sheikh Dahiru Bauci, Sarkin Musulmai, Sheikh Yahaya Jingir, Sheikh Khalid, Maitama Sule, Sani Zangon Daura, Ango Abdullahi,da sauransu, kuma dangantakata ya kara min sanin addinin Musulunci.” Inji Dalung
Daga karshe minista Dalung ya shawarci Musulmai da Kirista da su zauna lafiya da juna, sa’annan su kawar da kai daga dukkanin masu kulla rikici a tsakaninsu, kuma ya ce wannan lamari ya karfafa masa kwarin gwiwar ci gaba da kokarin samar da fahimtar juna tsakanin addinan biyu.

3 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here