TAMBAYOYI KAN AZUMI, TSARKI, JININ HAILA DA NA BIKI

2
8371
Daga DSP Imam Ahmad Adam Kutubi
Zone 7 Police Headquaters Wuse Zone 3, Abuja 08036095723
TAMBAYA TA 1: Shin mace mai jinin biki za ta zauna har kwana arba’in ne
ba za ta yi sallah ba kuma ba za ta yi azumi ba, ko kuma abin lura daga
gareta  za ta yi tsarki, ta yi sallah, kuma nawa ne mafi karancin
kwanakin da za ta yi kafin ta yi tsarki?
AMSA: Mace mai jinin biki ba ta da kaiyadadden lokaci sai dai duk
Iokacin da jinin ya zo mata za ta zauna ba za ta yi sallah ba kuma ba za
ta yi azumi ba kuma mijinta ba zai iya saduwa da ita ba. Amma idan ta ga
jinin ya dauke, wato ta tsarkaka ko da kafin ta cika kwana arba’in ne
ko da jinin iyakacin kwana goma kawai ya yi ko kwana biyar kawai sai ya
dauke, to sai ta yi wanka ta yi sallah, ta yi azumi kuma mijinta ya sadu da
ita babu laifi a cikin hakan.
    Sai dai abin da ya fi muhimmanci shi ne shi jinin biki al’amari ne
kebantacce kuma hukuncinsa yana ratayuwa ne da shi, wato idan jinin
ya zo to hukuncinsa yana nan ba za ta yi azumi da sallah ba. Kuma idan
jinin bai zo ba to hukuncinsa ba ya nan. Duk lokacin da ta yi tsarki to
ta wofanta daga hukuncinsa.
    Sai dai idan jinin ya karu matar ta zamo mai jinin Istihada, wato
jinin ciwo kenan, sai ta yi lissafln iya kwanakin al’adarta sai ta yi
wanka ta yi sallah. Sai ta nemi maganin wannan jinin na cuta.
TAMBAYA TA 2: – Mai tambaya yana cewa:- Mace ce bayan an yi mata aure
da wata biyu bayan ta yi al’ada ta yi tsarki sai kuma ta fara ganin wani
digon jini kadan; to shin wannan matar za ta sha azumi ne idan lokacin
azumi ne ko kuma mene ne za ta aikata?
AMSA:- Mas’alolin mata a cikin al’ada da aure kogi ne wanda ba shi da
iyaka sai dai ka’ida ta gaba daya cikakkiya ita ce idan mace ta
tsarkaka ta ga tsarki tabbatacce daga al’adarta – wato fitar wani farin
ruwa bayan daukewar jinin al’ada, to idan wani bakin jini ya zo bayan
ta ga wannan farin ruwan ko wani fatsi-fatsi ko wani dan digon jini ko
wani danshi to duk wannan abubuwan ba haida ba ne kuma ba ya hana azumi
da sallah da jima’i domin shi ba haida ba ne.
    Ummu Adiyya ta ce mu ba ma kirga baki da kankanin jini wani abu (wato ba
mu dauka haida ba). Bukhari ne ya fito da Hadisin. Abu Dauda kuma ya
kara da cewa idan bayan mace ta yi tsarki tabbataccen tsarki sai ta ga
daya cikin wadannan abubuwa to ba zai cutar da ita ba kuma ba zai
hana ta sallah da azumi da saduwa da mijinita ba.
    Sai dai yana wajaba a kan mace kada ta yi gaggawa wajen yin wanka har
sai ta ga tabbataccen tsarki domin wasu matan daga sun ga jini ya
bushe a gabansu sai su yi gaggawar yin wanka tun kafin su ga farin
ruwan ko daukewar jinin gaba daya. Don haka ne matan Sahabbai suke
aika wa wajen Uwar Muminai A\’isha, Allah Ya yarda da ita, suke aikawa
da auduga a jikin audigar kuma suna shafa jini sai ita kuma ta ce musu
kada ku yi gaggawa har sai kun ga farin ruwa sannan ku yi tsarki.
TAMBAYA TA 3:- Me tambaya yana cewa:- Mene ne hukuncin samuwar mace a
cikin Masallaci mai Alfarma alhalin tana haila don sauraron Hadisai da
khudubobi? ‘
AMSA:- Ba ya halatta ga mace mai haila ta zauna a cikin Masallaci mai
Alfarma ko wanin wannan masallacin daga cikin masallatai, sai dai yana
halatta a gareta ta wuce ta masallacin ko kuma ta dauki wani abu a
cikin masallacin da makamantan hakan, kamar yadda Annabi (SAW) ya ce wa
A\’isha yayin da ya umarce ta da ta dauko masa dardumar salla sai ta ce masa ai
dardumar tana masallaci ita kuma ga shi tana haila, sai Annabi (SAW)
ya ce mata ai hailar ba a hannunki take ba (wato za ta iya shiga
masallacin don ta dauko dardumar.
    Idan mace mai haila ta wuce ta cikin masallaci ta tabbatar cewa jinin
ba zai zuba ba a ciki ba, to babu laifi a kan haka.
    Amma idan tana nufin ta shiga ta zauna a masallacin ne to bai
halatta ba. Dalilin haka kuwa shi ne Annabi (SAW) ya umarci mata su fita
zuwa gurin sallah lokacin Sallar ldi ya umarci ‘yan mata da tsofaffi
da budurwaye da masu haila sai dai masu haila ya ce su fita daga cikin
filin sallah su je gefe.
    To wannan yana nuni a kan ba ya halatta ga mace mai haila ta zauna a
masallaci don sauraron huduba ko don sauraron darasi ko Hadisai.
TAMBAYA TA 4:- Shin yana wajaba ga mace mai jinin biki ta yi azumi,
ta yi sallah idan jini ya dauke mata kafin kwana arba’in?
AMSA:- ‘E’. Idan mace ta samu tsarki, jinin biki ya dauke mata kafin
kwana arba’in yana wajaba a gareta ta yi azumi idan ya kasance a cikin
Ramadana ne, kuma ya wajaba a gareta ta yi sallah.
    Kuma ya halatta ga mijinita ya sadu da ita. domin ta tsarkaka, ba ta
tare da abin da zai hana ta yin azumi da sallah kuma ya halatta a sadu
da ita.
TAMBAYA TA 5:- ldan wani digon jini kadan ya fito wa mace a ranar
Azumin Ramadana ita kuma matar tana azumi shin azuminta ya inganta?
AMSA: ‘E’. Azuminta ya inganta kuma wannan digon jini kankani ba komai
ba ne domin daga jijiya yake.
    Kuma Aliyu bin Abi Dalibi Allah ya yarda da shi ya ce: “wannan digon
jini kamar habo ne na hanci, ba haila ba ne, haka AIi ibn Abi Dalib ya
ambata (RA).
TAMBAYA TA 6:- ldan mace ta ji dumin jini amma jinin bai fito kafin
magariba ba, ko kuma ta ji radadi na ciwon al’ada amma kuma jinin bai
zo ba to shin azuminta na wannan ranar ya inganta ko kuma ya wajaba ta
rama?
AMSA:- Idan mace ta ji dumi na haila kuma tana azumi amma kuma hailan
bai fito ba sai bayan sallar magriba, ko kuma ta ji radadi na haila
amma kuma jinin bai zo ba sai bayan sallar magariba bayan fuduwar rana,
to azuminta na wannan rana ingantacce ne kuma ba za ta rama wannan
azumin ba in na farilla ne kuma ladar azumin bai baci ba idan azumin
ya kasance na nafila ne.
TAMBAYA TA 7:- ldan mace ta ga jini amma kuma ba ta tabbatar cewa jinin
haila ba ne to mene ne hukuncin azuminta a wannan rana?
AMSA:- Azuminta ya inganta a wannan rana domin asalin jinin ba na haila
ba ne, har sai lokacin da haila ne ya bayyana a gareta” sannan azuminta
zai baci.
TAMBAYA TA 8:- Wani lokaci mace tana ganin wani gurbi na jini dan
kadan ko kuma wani kankanin digon jini daban da wani lokaci fa gan shi
a lokacin al’adarta, wani lokaci, kuma ta gan shi ba a lokacin
al’adarta ba, to mene ne hukuncin azuminta a wadannan halaye guda biyu?
AMSA:- Amsar tambaya mai kama da wannan ta gabata a baya, sai dai idan
wannan digo ya zo ne a lokacin haidarta.
    Kuma ta lura da cewa yana daga cikin jinin al’ada wanda ta san shi to
wannan ya kasance haida.
TAMBAYA TA 9:- Idan mace ta ga jini a lokacin al’adarta, ta ga jini a
ranar farko amma a rana ta biyu ba ta ga jinin ba har tsawon wuni guda,
mene ne a kanta, mene ne za ta aikata?
AMSA:- Abin da yake zahiri shi ne lallai wannan tsarki ko kuma bushewar
jini da bai zubo ba, wanda ya auku ga wannan mata a kwanakin hailarta
to a lissafin haila yake ba a daukar shi tsarki, to don haka sai ta
wanzu a cikin hani na abin da mai haila take bari – kamar sallah, azumi
da sauransu.
    Amma sashin malamai sun ce:- wacce ta kasance tana ganin jini rana
daya washegari kuma ta ga babu jinin idan haka take yi to idan jinin ya
zo haida ne, idan kuma ya dauke tsarki ne, sai ta yi ta kirgawa har sai
ya kai kwana goma sha biyar, wato idan ya karu za ta kara kwana uku, idan
ya zarce ta yi wanka ta nemi magani. Idan wani watan ya zo za ta yi karin
kwana uku to idan ya kasance kowane wata tana yin karin kwana uku amma
jinin ba ya tsayawa har ya kasance ta zama mai al’adar kwana goma
sha biyar, to daga nan ba za ta sake yin karin ba idan wani wata ya zo
idan jinin ya wuce wadannan kwanakin sai ta yi wanka, ta yi sallah, ta
ci gaba da ibada sai ta nemi magani don ya zama jinin ciwo.
    Kuma shi wannan karin kwanaki da ake yi ba a lokaci daya ake yinsa ba
idan da mata tana yin kwana uku ne da wani watan ya zo sai ta ga ya wuce
kwana uku bai dauke ba to sai ta kara kwana uku ya zama kwana shida
kenen idan ya yi kwana shida bai tsaya ba sai ta yi wanka ta yi sallah ta
nemi magani. To idan wani watan ya zo ta zama mai al’adar kwana shida
kenan. Idan jinin ya yi kwana shida bai tsaya ba sai ta kara kwana uku
a kai ya zama kwana tara idan ta yi kwana tara jinin bai tsaya ba sai
ta yi wanka ta yi sallah. To haka za ta yi ta yin kari har zuwa lokacin
da zai kai kwana goma sha biyar daga nan kuma ba wani karin da za ta
dada a kai.
    Wannan shi ne zance mafi shahara a mazhabar, Ahmad bini Hanbali, Allah
ya jikansa.
TAMBAYA TA 10:- A rana ta karshe daga cikin ranakun haila amma kafin
ta yi tsarki matar ba ta ga gurbin na jinin haila ba, shin za ta yi
azumin wannan rana alhali kuma ba ta ga farin ruwa ba, ko kuma ya za ta
yi?
AMSA:- Idan ya kasance a al’adar matar ba ta ganin farin ruwa idan jini
ya dauke mata kamar yadda ake samun wasu daga cikin mata, idan jini ya
dauke musu ba sa ganin wannan farin ruwan daga baya, matar za ta yi
azumi.
Idan kuma ya kasance a karshen al’adar tana ganin farin ruwa idan jini
ya dauke mata to ba za ta yi azumi ba har sai ta ga wannan farin ruwan.
TAMBAYA TA 11:- Shin lallai ne mai haila ta canza tufafinta bayan ta yi
tsarki kuma ta san cewa jini bai taba tufafin ba kuma babu najasa a
jikin tufafin?
AMSA:- Ba lallai ba ne ta canja tufafinta domin shi jinin haida ba ya
bata jiki, shi dai jinin haida yana bata abin da ya taba ne kawai,
wato idan ya taba abu to sai ya zama najasa saboda haka ne Annabi
(SAW) ya umarci mata da su wanke tufafinsu idan jinin haila ya same shi
wato idan jinin ya taba shi kuma su yi sallah da tufafin bayan sun
wanke.
TAMBAYA TA 12:- Shin danshi da yake fito wa mace wannan danshin
tsarki ne ko najasa, Allah ya saka muku da alheri?
AMSA: Abin da yake sananne dai a gurin ma’abota ilimi shi ne dukkan
abin da yake fitowa daga hanyoyi guda biyu to najasa ne, sai dai abu
daya ne kawai ba najasa ba – shi ne maniyi. Shi dai maniyi abu mai
tsarki ne in kuwa ba shi ba to duk abin da yake fitowa ma’abocin
kazanta ne yake fitowa ta hanyoyi guda biyu. To wannan danshi najasa
ne kuma yana daga cikin abin da yake warware alwala kuma karin bayani
a kan wannan, ya kasance dukkan abin da yake fitowa mace na wannan ruwa
najasa ne kuma dole ne ta sake alwala. Wannan shi ne abin da aka samu
bayan an yi bincike tare da sashin malamai.
Sai dai ni ina da dan damuwa domin sashin mata suna kasancewa tare da
wannan danshi kodayaushe, to abin da za ta yi shi ne ta yi mu’amala irin
mu’amalar wanda yake da yoyon fitsari. Sai ta dinga yin alwala a
lokacin ko wacce sallah, idan lokacin sallah ya yi sai ta yi alwala ta yi
sallah.
TAMBAYA A KAN ALWALA
TAMBAYA TA 13:- Shin yana halatta nayi alwala alhalin a jikina ko
fatata akwai wani nau’i na maiko ko man shafawa?
AMSA:- ‘E”, yana halatta a gare ki ki yi Alwala ko da a jikinka akwai
irin wadannan man shafawa da sharadin wannan man bai kasance wanda zai
hana ruwa shiga jikin ka ba ne kamar (Janfarce). Idan kuma ya kasance
mai kauri ne wanda zai hana ruwan shiga fatar jikin wato kamar
(Janfarce) to ba makawa sai an cire shi kafin a yi alwala.
TAMBAYA TA 14:- Idan mace mai ciki ta ga wani jini kafin ta haihu da
kwana daya ko biyu), shin za ta bar yin azumi da sallah saboda wannan
jini ko ba za ta bari ba?
AMSA:- Idan mace mai ciki ta ga jini kafin ta haihu da kwana daya ko biyu
tare da ita akwai tabbacin cewa wannan jini na biki ne, to sai ta bar
yin sallah da azumi a dalilin wannan jini.
    Idan kuma babu wata alama da ta nuna ya yi kama da na biki, wato idan
ba jinin biki ba ne, to wannan jinin ya zama gurbataccen jini ba zai
hana yin sallah da azumi ba.
TAMBAYA TA 15:- Mene ne Haila?
AMSA:- Haila shi wani jini ne da yake fita da kansa daga gaban mace.
wace za ta iya daukan ciki.
TAMBAYA TA 16:- Kashi nawa ne mata suka kasu dangane da haila?
AMSA:- Mata sun kasu kashi uku: (1) Wacce ta fara (2) Wacce ta saba
(3) Mai ciki.
TAMBAYA TA 17: Nawa ne mafi yawan kwanakin haila ga wacce ta fara?
AMSA:- Mafi yawan kwanakin haila ga wacce ta fara kwana goma sha biyar ne (15).
TAMBAYA TA 18:- Mene ne hukuncin wacce ta saba yin haila?
AMSA:- Wacce ta saba al’ada ta san kwanakinta
    Amma idan jinin ya wuce mata ya karu a kan kwanakin da ta saba, to sai
ta kara kwana uku matukar karin ka da ya wuce kwana goma sha biyar.
    Kuma na yi bayanin yadda za ta yi karin kwanaki a kowane wata. Na yi
bayani a baya.
TAMBAYA TA 19:- Mene ne hukuncin mai ciki?
AMSA:- Hailar mai ciki bayan ya yi wata uku to hailar ta kwana goma sha biyar ko kafin sha biyar. Amma bayan ciki ya yi wata shida kwana ashirin ne, wato mafi yawan
kwanakin hailar. Amma in ya wuce hakan to ya zama jinin ciwo, sai ta yi
wanka ta ci gaba da ibadarta kamar yadda bayani ya gabata a baya.
TAMBAYA TA  20:- Mene ne hukuncin mata idan jinin ya dauke?
AMSA:- Idan jinin ya dauke sai ta kirga kwanakinsa har sai ta cika
al’adarta kamar yadda ta saba wato idan jini ya dauke kafin ya kai
kwanakin da ya saba yi mata sai kuma ya dawo to sai ta dinga kirga
kwanakin har sai ya kai iya kwanakin da ta saba yi. Kamar jinin ya zo
yau sai ya dauke gobe sai kuma ya dawo jibi, to sai ta hada na yau
da na jibin ya zama kwana biyu kenan to haka za ta yi ta lissafi har sai
ya cika kwannakin da ta saba.
TAMBAYA TA 21:- Shin yana halatta ga mai haila ta yi sallah da makamantan sallar?
AMSA:- Ba ya halatta ga mai haila ta yi sallah da azumi da dawafi da shafar Alkur’ani da shiga masallaci.
TAMBAYA TA 22:- Shin za ta rama daga cikin sallah ko a azumi?
AMSA:- Za ta rama azumi amma ban da sallah.
TAMBAYA TA 23 :- Shin karatunta wato (mai haila ya halatta?
AMSA:- “E”, karatunta ya halatta
TAMBAYA TA  24:- Mene ne a jikinta ba ya halatta ga mijinta a lokacin da
take haila?
AMSA: Farjinita ne ba ya halatta ga mijinta, kuma abin da yake
tsakanin cibiyarta zuwa gwiwoyinta a lokacin da take haila, har sai
ta yi wankan tsarki, wato wankan daukewar jinin haida.
T AMBAYA  TA 25:- Mene ne Nifasi?
AMSA:- Shi nifasi shi ne wani jini da yake fitowa a lokaci haihuwa.
TAMBAYA TA 26:- Shin nifasi wato jinin biki kamar jinin haila yake a
wajen hukunci?
AMSA:- Jinin biki kamar jinin haila yake wajen haninsa, wato duk abinda ake bari idan jinin haila yazo to haka ake bari idan jinin biki ya zo kamar barin sallah da azwni da sauran ibada.
TAMBAYA TA 27:- Nawa ne mafi yawan kwanakin jinin biki?
AMSA:- Mafi yawan kwanakin jinin biki kwana sittin ne (60).
TAMBAYA  TA 28:- To mene ne hukuncin mace idan jinin biki ya yanke mata
kafin ta cika kwanna sittin.
AMSA:-  Idan jinin ya dauke mata kafin ta cika kwana sittin to sai
ta yi wanka ta yi sallah ta yi azumi, idan lokacin azumi ne, kuma mijinta
zai iya saduwa da ita tun da ta tsarkaka.
TAMBAYA TA 29:- Sannan kuma mene ne za ta aikata idan jinin bikin ya dawo mata?
AMSA: Idan jinin ya dawo mata, idan ya kasance tsakaninsa da na baya
wanda ya dauke din nan kwana goma sha biyar ne tsakaninsu ko kuma ya
fi kwana goma sha biyar sai ya dawo, to na biyun nan haida ne.
    Idan kuma tsakanin na farko da na biyun, wanda ya dawo bai kai kwana
goma sha biyu ba, to sai ta hada lissafin kwanakin da, da farko ya
kasance daga cikan lissafin kwanakin jinin biki.
TAMBAYOYI A KAN AZUMI DANGANE DA MAI JININ HAILA KO BIKI
TAMBAYA TA 30:- Shin mace mai jinin haila da  mai jinin biki za su ci
abinci su sha abin sha lokacin Azumin Ramadana?
AMSA: “E”.  Za su ci su sha abin sha a  Azumin Ramarlana, sai dai
abin da ya fi kyau hakan ya zamo a asirce, idan ya kasance akwai wani
daga cikin yara tare da wannan matar a cikin gida, domin cin abincin
matar da kuma shan abin shan nata zai rikitar da yara, to don haka sai
ta ci a boye kar yaran su gani. Bayan ya dauke sai ta rama azumin da ta
sha.
TAMBAYA TA 31:- Mene ne ra’ayin ka dangane da shan kwayoyi na hana
jinin haila wanda yake zuwa a mata duk wata, mene ne ra’ayinka dangane
da kwayoyin da ake sha don hana wannan wai don matan su samu su yi
azumi tare da mutane,  don kar su sha azumi?
AMSA:- Ni dai ina gargadi ina tsoratarwa daga shan wannan kwaya, akwai
cutarwa a cikinta cutarwa mai girma. Kuma na tabbatar da hakan ta gurin likitoci.
    Kuma abin da za a gaya wa mata shi ne:­ Wannan jini Allah ne ya
rubuta wa ‘yan Adam don haka su yarda da abin da Allah ya rubuta kuma
su yi azumi a lokacin da babu abin da zai hana su yin azumin. Idan kuma
ya zo lokacin da suke da abin da zai hana su yin azumin to su sha
azumin suna masu yarda da abin da Allah mai Girma da Daukaka ya
kaddara.
TAMBAYA TA 32:- Mene ne hukuncin dandana abinci lokacin Azumin Ramadana
alhalin matar kuma tana azumi?
AMSA:- Hukuncinsa babu laifi da shi idan dai akwai wata bukata da ta
janyo zuwa ga yin hakan, sai dai matar kuma ta tofar da abin da ta
dandana da sauri kuma kar ta bari ya shiga cikin makwogwaronta.
TAMBAYA TA  33:- Idan mace hailarta ta yanke kafin fitowar Alfijir
amma ba ta yi wanka ba sai bayan fitowar alfijir yaya azuminta?
AMSA: Idan mace jinin ta ya yanke kafin fitowar Alfijir ko da da minti
daya ne matukar ta tabbartar da jinin ya yanke da auduga ko da farin
kyale to azuminta bai baci ba. Don ta yi azumi ne lokacin da jininta ya
dauke. Kodayake ba ta yi wanka ba sai da Alfijir ya keto, to ba komai
a kanta, hakanan kuma da za ta wayi gari da janaba amma ba ta yi wanka ba
sai bayan fitowar Alfijir to Azumin ya yi.
    Da wannan ne na ke so na ja hankalin mata don wasun su sukan yi bude
baki bayan rana ta fadi amma ba su yi sallah ba sai jini ya zo musu suna
gani kamar ba su da wannan azumin. Wannan magana tasu ba ta da asali
tun da ta riga ta sha ruwa kuma rana ta fadi, ko da minti daya ne sai
jini ya zo mata to babu abin da ya shafi azuminta.
TAMBAYA TA 34:- Idan mace mai jini biki jininta ya yanke kafin a kwana
arba’in (40) shin ya halatta ta yi azumi ta yi sallah?
AMSA:- ‘E’, ya halatta duk lokacin da jini ya dauke wa mace bayan
haihuwarta tilas ta yi wanka in a watan Azumi ne ta ci gaba da azuminta
don ta tsarkaka. Don haka babu abin da zai hana sallah da azumi da kuma
saduwa da mijinta.
TAMBAYA TA 35:-  ldan mace al’adarta kwana bakwai ko takwas sannan
jinin ya karu da kwana daya ko kwanuka biyu, to mene ne hukuncinta?
AMSA:- ldan mace al’adarta kwana shida ne, ko bakwai ko takwas daga
shida sai ya ki tsayawa ya kai kwana bakwai, ko takwas ko tara, ko
kwana goma, kai ko kwana goma sha daya. To za ta bar sallah da azumi,
har sai jinin ya dauke. Don Annabi (S.A.W) bai iyakance iyakarsa ba ya
danganta ne da gwargwadon al’adar da mace take yi. Don haka ne ma
Allah (S.W.T.) Yake cewa: “Suna  tambayarka mene ne hukuncin haila, sai
Allah Ya ce ka ce  kazanta ce\’\’. Kula da wannan ayah. Duk lokacin da mace
take tare da wannan jini dole ne ta bar sallah har sai ta yi wanka. In
ya ragu a gwargwadon da take yi shi kenan. In kuma ya kara karuwa,
matukar bai wuce kwana goma sha biyar ba. Amma ba a lokaci daya ake
karin ba kamar yadda ya gabata.
TAMBAYA TA 36: Wai tilas ne mace mai jinin biki ta zauna ba sallah,
ba ta azumi har kwana arba’in? Ko kuma in ya yanke kafin kwana arba’in
tana iya yin sallah da azumi?
AMSA: – Mace mai jinin biki ba wai sai ta kai kwana arba’in ba. ldan
jinin ya yanke, ko bayan kwana goma ne ko kwana biyar sai ta yi wanka,
ta yi azumi, ta yi saIlah, har ma mijinta ya saduwa da ita. Ko da a ranar
da ta haihu ya dauke sai ta yi wanka ta yi sallah.
TAMBAYA TA 37:- Idan mace taga dan digon jini kadan sai taci gaba da
Azuminta har zuwa karshen Watan Azumi, shin azuminta nabnan?
AMSA:- ‘E’, Azumin ta yayi, don wannan jini dan digonnan ba komai ba
ne. Wannan jini yana daga jijiya ne. Don Hadisin da aka karbo daga
Aliyu dan Abi Talib (RA) yace irin wannan digon habo ne kawai dake
fitowa daga hanci ba haida bane, haka  aka karbo daga Aliyu (RA).
TAMBAYA TA 38:- Idan mace mai haila, ko biki jininta ya dauke kafin
fitowar Al-fijir, amma bata yi wanka ba sai bayan fitowar Al-fijir,
shin Azuminta yayi?
AMSA:- ‘E’, Azumnta na nan, idan dai har tayi tsarki kafin fitowar
Al-fijir haka yake ga mace mai haida da mai biki, don wadannan suna
daga cikin wanda Azumi ya wajaba a kansu. Don kamar wanda ya wayi gari
ne da janaba, amma bai yi wanka. Don Allah (SWT) Yana cewa a cikin
Al-Kur’ani  Mai  Girma, yanzu mun halarta muku ku sadu da matayenku a
cikin daren Ramadana don neman abin da Allah (SWT) ya rubuta muku na
arziki. Kuma kuci, ku sha har sai bakin zare (wato fitowar Al-fijir).
To tun da Allah (SWT) yayi izini ana iya saduwa da iyali har zuwa
fitowar Al-fijir kaga kenan wanka sai bayan Al-fijir ya keto. Sabo da
Hadisin Aisha (RA), Annabi yana wayan gari da janaba wanda ya sadu da
iyalensa. Wannan ya nuna Annabi (SAW) ba ya wanka sai bayan fitowar
AI-fijir.
TAMBAYA  TA 39:- ldan mace taji alamun jini amma bai fito ba, ko dan
dumi amma bai fito ba da ta duba, shin Azumin ta yayi? Ko zata rama?
AMSA:- Idan mace taji alamun jini ko dumi, amma bai fito ba, da ta
duba bata ga jini ba amma ga shi tana Azumi, amma bai fito ba sai
bayan faduwar rana to, Azuminta bai baci ba. Tun da jini bai fito ba
sai bayan rana ta fadi.
TAMBAYA TA 40:- Idan mace taga jini amma bata san a’ina ta same shi
ba, to menene hukuncin Azuminta?
AMSA:- Azuminta na wannan rana bai baci ba. Idan ta duba da wani
kyalle ko auduga kuma dai ba haida take yi ba har sai ta sami hujja
kwakkwara don asali ta dauka ba haida bane.
TAMBAYA TA 41:- Wani lokaci mace tana ganin digon jini kadan, a waje
waje a jikin tufarta da rana; wani lokaci tana ganin haka lokacin
al’adarta, wani lokaci ba lokacin al’adartaba, to menene hukuncinta a
wannan lokaci biyu, ko halaye biyu?
AMSA:- Irin wannan tambaya mun amsa ta a baya to amma in taga wannan
digon jini a ranakun al’adarta, to wannan ba tababa haidane, ba tada
Azumin wannan rana.
TAMBAYA TA 42:- Mace mai haila ko jinin biki zata iya ci da sha da ranan Azumi?
AMSA:- ‘E’, zata iya ci da sha meye zai hana, amma taci a boye in
akwai yara a gidan,don karya rikita yara kanana.
TAMBAYA TA 43:- In jini ya yanke a lokacin Sallar La’asar shin Azahar
da La’asar ne zata yi ko La’asar ne kawai?
AMSA:- Maluma sun yi sabani, wasunsu sun ce Azahar da La’asar ne zata
yi, wasu suka ce babu wani dalilin wajibcin Azahar a kanta. Don
lokacin jini bai yanke ba, don Annabi (SAW) ) ya ce wanda ya riski
raka’ah daya a Sallah La’asar, kafin rana ta fadi, to hakika ya riski
Sallar La’asar. A wannan Hadisin a lura yace ta riski La’asar, bai ce
ta riski Azahar da La’asar ba, sai ya ambaci La’asar kawai.
TAMBAYA TA  44:- Idan mace a lokacin da take al’ada, sai taga jini
Iokacin al’adarta, sai ya yanke a kwana daya meye hukuncinta?
AMSA:- Idan mace taga jini a kwana daya, rana na biyu bata gani ba to
wannan bushewar gaban tane amma tana nan, sai ta zauna kar tayi
SalIah, kar tayi Azumi.Wasu malamai sukace, in jinin zai zo kwana daya
sannan kwana na biyu sai ya dauke, to ranar da ya dauke tayi tsarki
sai tayi wanka taci gaba da SalIah da Azumi, in kuma ya dawo to sai ta
ajiye Azumi da Sallah. Har ya kai gwargwadon kwanakin da take ganin
jini matukar bai wuce kwana goma sha biyar ba, in ya wuce kwana goma
sha biyar, to ciwo ne sai ta nemi magani ta cigaba da Sallah da Azumi.
ABIN YI IDAN WANKAN JANABA DA NA BIKI SUKA HADU KAN MACE
TAMBAYA TA 45:- Mijinane ya sadu dani da naje wankan janaba sai na ga
jinin haila yazo min to yaya zanyi?
AMSA:- Wanda mijinta ya sadu da ita dataje wankan janaba sai taga jini
yazo mata ba zatayi wankan janaba ba sai ta tsaya sai wannan jinin ya
dauke sai tayi wanka daya da niyya biyu. Niyya ta farka don wankan
janaba sannan kuma daga baya tayi niyyar wankan haida.
TAMBAYA TA 46:- Mace bata yi Sallar Azahar ba Iokacin Salar La’asar ta
dauki buta za tayi alwala sai jini yazo mata. To idan jinin ya dauke
zata yi Azahar da La’asar ne ko meye hukuncinta?
AMSA:- Idan mace ba tayi Sallar Azahar ba  har Iokacin Sallar La’asar
ya shiga to idan jinin ya dauke zata biya Sallar Azahar ne kawai banda
La’asar don Iokacin sallar La’asar jini yazo mata, mai jini kuma
lokacin da take jini babu Sallah akanta
TAMBAYA TA  47:- Karshen daukewan jinin mace sai bata ga jini ba kuma
bata ga farin ruwa ba, me zata yi?
AMSA:- In ya zama al’adarta ya dauke kamar yadda wasu mata suke, to
shikenan sai taci gaba da Azumi. Amma in ya zama al’adarta tana ganin
farin ruwa duk lokacin da jini ya dauke to baza tayi Azumi ba sai taga
wannan farin ruwa.
HUKUNCI KAN DALIBA MAI AL’ADA DA KARATUN AL-QUR’ANI
TAMBAYA TA  48:- Menene hukuncin mace mai al’ada ta karanta Qur’ani,
ko da ka ko ta rike Qur’ani a halin lalura ga shi ita kuma  dalibace.
Shin ya halatta ta karanta Kur’ani da ka ko da littafi?
AMSA:- Babu laifi ga mai haila ko jinin biki ta karanta Qur’ani kan ta
haddace kamar malama ko mai karantarwa. Wacce kullum sai ta karanta
wani juzu’i da dare ko rana, babu laifi saboda lalura. Amma don neman
lada bai halarta. Don mafi yawan malamai suna ganin mai haila ko mai
biki bai halarta ta karanta Kur’ani ba.
TAMBAYA TA  49:- Mace mai haila ko biki zata iya canza kayanta, tare
da tasan cewa jini bai shafi kayanta ba, shin dole ne sai ta kwabe
kayan?
AMSA:- Ba wai sai ta canja kayanta ba don  jini baya bata shi, yakan
bata inda ya taba ne. Don haka Annabi (SAW) ya umarci mata in suka ga
jini a tufarsu, sai su wanke inda ya taba, suyi Sallah da tufar.
MATAR DA BIYAN BASHIN AZUMIN RAMADANA NA SHEKARU SUKA KAMA TA
TAMBAYA TA 50:- Mace ne ta sha Azumin kwana bakwai lokacin da take
biki, har wani  Ramadana yazo bata biya ba har kuma cikin Ramadana na
biyu shi ma ta sha na kwana bakwai, kuma ya zamo tana ciyarwa saboda
rashin lafiya wanda take tare da shi. Sannan ga Ramadana na uku ya
kusa zuwa, to menene hukuncin ta?
AMSA:- Kar mace ta zama kamar yadda tambayar yake, wato in bata da
lafiyane babu damuwa, lokacin da ta sami lafiya sai ta biya na
shekarar can baya dana bara amma idan sakaci ne to, bai halarta a
gareta fa sha Azum,i ta sake bata biya ba, har wani Ramadana yazo bata
biya ba. In kuma tayi haka to tayi laifi. An sami Hadisi daga A’isha
(RA), ta ce “ya kasance Annabi yana Azumi amma bana iya biya sai an
shiga watan Sha’aban to idan muka lura da wannan Hadisi na A’isha (RA)
yana nuna duk cewa yanda za’ayi mutum ya biya kafin Ramadan. To ita
wannan mata ta duba ta gani in da ganganne tayi gaggawan tuba ga Allah
(SWT) ta kuma biya abin da ake binta. In kuma rashin lafiya ne, to
Allah Ya sani, Shi Ya sa ta jinkirta shekara daya ko biyu, to babu
laifi duk, lokacin da ta sami lafiya, sai ta rama abin da ake binta na
ramuwa.
TAMBAYA TA 51:- Mace ne tasha Azumi, amma bata rama ba kuma ga sabon Azumi yazo?
AMSA:- Wanda ta jinkirta ba ta rama ba har wani Ramadan yazo, ro ta
tuba ga Allah (SWA) da wannan mummunan aiki da tayi don bai halarta ba
mutum yayi jinkirin biyan Azumi har wani Azumi yazo. Don A isha (RA)
tace: Anabina Azumin watan Ramadana amma bana biya sai a watan
Sha’aban. Wannan Hadisi na A’isha (RA) bai halatta ga mutum yayi
jinkirin abinda ake binsa na Azumi har wani Ramadan yazo ba. Don haka
ta tuba zuwa ga Allah (SWT), in sabon Azumin ya wuce ta biya amma zata
ciyar gwargwadon Azumin da ta sha, amma ya wuce ta rama.
HUKUNCI KAN SHAN  MAGANIN HANA HAILA DON YIN AZUMI
TAMBAYA TA 52:- Menene ra’ayinku akan mace ta sha kwayan hana ganin
jini don ta sami Azumi tare da jama’a?
AMSA:- Ina tsoratar da wacce zata yi haka don wannan kwayoyi yana
cutarwa sosai. Domin likitoci sun yi bincike, yana cutar da mahaifa;
kan an hana jini fita kuma yana cutar da jijiyoyi, kuma yana cutar da
jinin jiki don wannan jini Allah (SWT) shi ya kaddara wa mata ya fita
to, hana shi illa ne babba don haka ne muke gani kiyi Azumi kawai
lokacin da kika sami daman yi amma in jini ya zo ki barshi ya fito in
kin yi haka kin yarda da kaddaran Allah kenan. Bayan ya wuce sai ki
rama.
TAMBAYA TA 53:- Wannene yafi, mace tayi Sallah a dakin tane, ko ta
tafi masallaci, In ya zamo akwai wa’azuzzuka da tunatar wa?
AMSA:- Abin da yafi, mace tayi Sallah a dakinta, saboda hadisin Annabi
(SAW), da yake cewa: gidajen mata shi yafi alkairi suyi SaIlah a ciki
don fitan mata akwai fitina a ciki. Don haka mace ta zauna a dakinta
yafi mata aIkairi. Dangane da wa’azi kuma da ta ji a masallaci da
nasiha ta samu cassette ta sanya a dakinta yafi.
TAMBAYA TA 54:- Yaya dandana abinci ga mace mai Azumi da rana, don
taji ko gishiri yo ji?
AMSA:- Idan har an dandana ba a hadiye ba, aka tofar, wani abu bai
wuce makogwaro ba, to babu damuwa, Azumi bai karye ba.
TAMBAYA TA 55:- Ni mace ce, cikina nayi bari a wata uku tun shekara
guda banyi Sallah ba bar sai dana yi tsarki, sai aka ce min dole ne
sai na biya wadancan salloli ni kuma ban san yawan su ba?
AMSA:- Abin da yake sananne ga malamai, in cikinta ya zuba da wata
uku, idan halittarta uku na mutum cikakke, to wannan jini daya biyo
jinine na nifasi (wato haihuwa) ba za tayi Sallah ba, baza tayi Azumi
ba, idan kuma halittar bata cika ba wannan jini na ciwo ne, sai ta
cigaba da SalIah, amma ta nemi magani. To sai ta yi tunani. in cikin
ya zube ne ko tayi bari, in ya kai kwana tamanin (80) sai ta biya
Sallar kwana tamanin in kuma ba za ta iya sanin kwanakin ba, to sai ta
yi tayin SalIah har sai ta sakankance ta biya Sallah da ake bin ta.

2 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here