An Tsayar Da Yin Tashe A Jihar Kano

0
897

Mustapha Imrana Abdullahi

RUNDUNAR \’yan sandan Jihar Kano ta sanar da hana yin wasannin tashe a duk fadin jihar baki daya.

Rundunar ta bakin kakakinta Magaji Musa Majiya ta bayyana sanarwar cewa daukar wannan mataki ya biyo bayan rahotannin da aka samu cewa wasu batagari za su yi amfani da wasan tashen domin yin amfani da \’yan daba su tayar da hankalin jama\’a lamarin da zai kawo matsalar tsaro.
Idan dai ba a manta ba ko a jamhuriya ta biyu an taba aiwatar da irin wannan hanin kuma shi ma duk batu ne na tsaro da \’yan daba suka so yin amfani da shi.
Shi dai tashe wadansu wasannin al\’ada ne da ake amfani da su domin nuna al\’adu na Hausawa a dukkan shekara idan watan aazumi ya kai goma ana samun manya da yara su rika yi a cikin gidaje da wuraren zaman jama\’a a.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here