GWAMNA EL-RUFA\’I YA KADDAMAR DA SAYAR DA TAKI NA DAMINAR BANA A GARIN SAMINAKA

0
666
Isah Ahmed, Jos
GWAMNAN Jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmad El-Rufa\’i ya kaddamar da shirin sayar da takin zamani ga manoman jihar  na daminar bana, a ranar Talatar da ta gabata a garin Saminaka da ke karamar hukumar Lere.
Da yake jawabi a lokacin da yake kaddamar da shirin sayar da takin Gwamna Nasiru El-Rufa\’i ya bayyana cewa don ganin  manoman jihar sun sami amfanin gona mai tarin yawa a daminar bana. Gwamnatin jihar ta hada hannu da gwamnatin tarayya kan shirin samar da taki na fadar shugaban kasa don ganin an samarwa manoman jihar wadatatcen takin.
Ya ce  gwamnatin jihar tana bai wa harkokin bunkasa noma matukar muhimmanci ta hanyar samar da taki da irin shuka da magungunan feshi da injinan noma.
Gwamnan wanda shugaban majalisar dokoki ta Jihar Kaduna Honarabul Aminu Abdullahi Shagali ya wakilta ya yi bayanin cewa a shekaru biyu da gwamnatin jihar ta yi a kan mulkin jihar, ta gudanar da ayyuka da dama na bunkasa harkokin noma a jihar.
Ya ce gwamnatin jihar ta bayar da kwangilar aikin noman rani na garuruwan Panbeguwa da Galma tare da kirkiro shirin noman alkama a garin Ruwan Sanyi da ke karamar hukumar Kubau.
Tun da farko a nasa jawabin Kantoman karamar hukumar Lere Dokta Yusuf Saleh ya bayyana farin cikin al\’ummar karamar hukumar Lere, kan yadda aka kaddamar da wannan sayar da taki na bana a karamar hukumar. Ya ce babu shakka wannan wata babbar dama ce ga al\’ummar karamar hukumar wadda za su yi amfani da ita wajen bunkasa noma a karamar hukumar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here