GWAMNA SHETTIMA YA YI KAKKAUSAR SUKA A KAN WA\’ADIN DA YAN AREWA SUKA BA INYAMURAI

0
632
Daga Usman Nasidi
GWAMNAN Jihar Borno Kashim Shetima ya ce duk wanda yake kiran masifa ko yaki tabas bai san su ba ne.
Shattima ya ce duk wanda ya san yaki ba zai yi irin kalamun da matasan arewa suka yi ba na cewa kabilar Igbo su bar jihohin arewa.
Gwamnan ya ci gaba da cewa idan matasan arewa ba su san ma\’anar rashin zaman lafiya ba su nemi wani a jihar Borno ya yi masu bayani.
A matsayinsa na shuagaban kungiyyar gwamnonnin Arewa 19 ya ce yana ganin wadanda suka ba mutane wa\’adin ficewa daga kasarmu suna neman su tada fitina basu san yaki ba ne idan ba haka ba matasan arewa ba za su yi furucin da suka yi ba.
A kan fadin ra\’ayi gwamnan Borno Kashim Shetima ya ce akwai banbanci da kokarin tada fitina kamar yadda matasan Arewa suke neman yi da bayyana ra\’ayi.
Gwamnan ya ci gaba da cewa duk wanda yake neman tada zaune tsaye bai san tashin hankali ko yaki ba ne. Yana mai cewa duk wanda ya san yaki ba zai yi irin kalamun da matasan arewa suka yi ba na cewa kabilar Igbo su bar jihohin arewa nan da watanni uku.
Haka kuma \’yan sanda sun ba ‘yan kabilar Igbo mazauna Kano tabbacin samun kariya da ya dace
A cewar Gwamna Shettima yau idan akwai wanda ya fi kowa sanin masifar dake tattare da rashin zaman lafiya shi ya fi kowa sani a matsayinsa na kasancewa gwamnan jihar Borno mahaifar \’yan ta\’addanci Boko Haram.
Yace idan yaro yace bai iya gudu ba bai ga abun gudu ba ne. Ya ce idan matasan arewa ba su san ma\’anar rashin zaman lafiya ba su nemi wani a jihar Borno ya yi masu bayani.
Ya ce a matsayinsu na kasancewa shugabannin a arewa idan sun ga abin da zai kawo tashin hankali da rashin zaman lafiya dole ne su tsawata saboda banbancinsu kenan da sauran kasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here