MATAR MAI GARKUWA DA MUTUNE EVANS TANA NEMAN AFUWAR GWAMNATI

0
800
Daga Usman Nasidi
UWARGIDAN babban Biloniyan nan mai garkuwa da mutane, Chikwudubem Onwuamadike, a.k.a Evans, ta ce tana zargin kishiyar mahaifiyar mijinta da yi masa asiri tun yana shekara 4 da haihuwa.
\’Yar shekara 31 ta yi wannan bayani ne yayin da ta yi hira da jarida Vanguard inda ta yi magana a kan damke mijinta da hukumar \’yan sandan Legas ta yi.
Tana miko kokon rokonta ga gwamnatin tarayya su taimaka su saki mijinta kana kuma wadanda ya taba yin garkuwa da mutanensu su yi masa afuwa.
Ta ce: “ Ina zargin kishiyar mahaifiyarsa da yi masa asiri. Ban san abin da ta yi masa yana karami ba amma ya fada mana. “Ina rokon gwamnati ta yafe masa, a yanzu da nike magana ina tsugunne da yarana muna kukan neman gafara. Ku ji tausayinmu. Bai san abin da yake yi ba. Na shirya dawowa Najeriya domin roko. Abin da nike karantawa a labarai na da ban tsoro\’\’.
“Duk da cewan ban samu labarin ya kashe kowa ba amma duk wadanda ya ji wa rauni da kuma ya dauki kudadensu su yafe masa saboda ni da yarana. Su yafe masa zai tuba ga ubangijinsa.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here