Alluran Rigakafin Jarirai Sun Kare -Inji Dokta Garba

0
777

Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna

SHUGABAN kungiyar masu asibitoci masu zaman kansu reshen Jihar Bauci Dakta Hassan Muhammad Garba, ya bayyana wa manema labarai cewa rigakafin maganin cutar Tarin Fuka da ake ba yaran da ake haihuwa a asibitoci a yanzu haka duk alluran sun kare baki daya.
Ya dai bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da kafar yada labarai ta BBC. Inda ya bayyana cewa hakika wannan al\’amari na karewar alluran rigakafin da ake yi wa jarirai a asibitoci abin damuwa ne kwarai domin ana son a yi masu ne da zarar an haife su kafin su bar asibitin da aka haife su zuwa gidajensu.
\”Mun yi kokarin yin tambayoyi da bincike ko za a samu amma duk a halin yanzu lamarin babu komai sai dai babu kawai, kodayake allura ce da ake kawowa daga wasu kasashen duniya amma a yanzu duk sun kare\”.
Don haka muna kira ga gwamnati da duk hukumomin da lamarin ya shafa da a yi kokarin daukar mataki kafin ya zama wani abu daban.
A halin yanzu ya tabbatar da cewa suna ba jama\’a hakuri ne kawai idan sun haihu a asibitoci su tafi gida.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here