AN SAMU SASSAN MUTANE A GIDAN WANI TSOHO MAI SHEKARU 80

0
873
Daga Usman Nasidi
TSOHON kauyen Gbogan wanda ke karkashin karamar hukumar Ayedade a Jihar Osun na cikin wani sabon tashin hankalin a yayin da aka samu rubabbun sassan jikin mutane a cikin wani gida a garin.
Rubabbun kawunan mutane 3 tare da wasu sassan jikin mutane daban-daban an gan su ne a cikin wani gida mai dakuna 4 a Idifa ta filin Ile-Eesu da ke Gbogan.
An samu gano rubabbun sassan mutanen ne sanadiyyar masifar wari da ta addabi jama’a da ke yankin, wadanda suka janyo hankalin mutane mazauna yankin zuwa ga gidan, wanda hakan kuma ya sa aka gudunar da bincike a kan gidan.
Majiyarmu ta samu labarin cewa a lokacin da wasu matasa suka shiga gidan wanda gidan wani mutumi ne mai shekara 80 a duniya, mai suna Lamidi Abioye wanda shi ke zama a cikin gidan shi kadai suka yi kicibis da ya baza sassan mutane a ko ina cikin gidan.
A yanzu haka an mika shi tsohon hannun ‘yan sanda sannan kuma rubabbun sassan mutane da aka samu a gidan na wurin su a matsayin shaida.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda reshen Jihar Osun, SP Folasade Odoro ya ce wanda ake zargin ya bayyana cewa shi mai maganin gargajiya ne.
Odoro ya tabbatar da cewa za a gudunar da bincike na musamman game da al\’amarin sannan kuma shi kuma wanda ake zargi za a shigar da karar shi don a yi mashi shari’a kamar yadda doka ta tsara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here