Ba Da Wa’adin Kungiyar Matasan Arewa Ga Igbo Babban Kuskure Ne –Sarkin Igbo

0
724

Muhammad Saleh, Daga Yola

SARKIN Igbo mazauna Yola fadar jihar Adamawa, Igwe Godwin Omenka, Eze Igbo III ya bayyana matakin da kungiyar matasan arewacin Najeriya na ba da wa’adi ga al\’ummar Igbo da cewa babban kuskure ne.

Da yake magana da manema labarai a Yola Eze Igbo III, ya ce matasan na arewa sun mance da cewa al\’ummar Igbo wani bangaren kasar dama bangaren arewacin kasar ne. 

“Igbo su fece daga Adamawa da jihohin arewa? Su ma wani bangaren jama’ar yankin da al’adun arewa ne ba bakin haure ba ne.

“Najeriya kasarmu ta gado ce, mu \’ya\’ya da jikokin wannan muhimmiyar kasa mu bar ta mu tafi ina? Igbo ‘yan kasa ne a kowace jiha, domin su wani bangaren ci gaban jihar ne.

“idan mun tafi kudu, mun zama baki a can, arewa ita ce gidanmu, mafiya yawanmu a nan aka haife su sun tashi a nan arewa, a nan muka yi makaranta a nan muka yi aure, muna da kyakkyawan dangantaka kuma mu haifuwar nan ne, mu Igbon arewa ne” inji Eze.  

Shugaban al\’umman Igbo da ke jihar Adamawa ya kuma yi kira ga jama’ar Igbo da ke harkokin kasuwanci a yankin da cewa su ci gaba da harkokinsu kamar yadda suka saba, ya ce “ku ci gaba da kasuwancinku kamar ba abin da ya faru, saboda a gida kuke.

“mutanen Igbo mutane ne masu son zaman lafiya, ku ci gaba da ba da gudumuwar ci gaba duk inda ka samu kanka” inji Igwe

Shugaban ya kuma bukaci gwamnatin tarayya da ma ta jihohi da su dauki matakin kare dukiyoyi da rayukan jama’ar Igbo, ya ce bai kamata wasu su yi amfani da wannan dama wajen lalata mausu dukiyoyi ba, ya yi addu’ar samun zaman lafiyar kasar nan baki daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here