A\’isha Buhari Ta Nemi A Ci Gaba Da Aiwatar Da Dabi\’un Watan Ramadan

0
744

 

 Zubair A Sada, Daga Kaduna
UWARGIDAN shugaban kasar Najeriya, Hajiya A\’isha Buhari a yau ta kammala azumin watan Ramadan da addu\’o\’i a filin Idi na \’Guards Brigade Mambila, Abuja. An fara sallar Idin ne da misalin karfe 9.30 na safe inda Babban limamin masallacin, Manjo Hamisu Mustapha ya jagoranci sallar.
A sakonta ga \’yan Najeriya, uwargida A\’isha Buhari ta gode wa \’yan Najeriya ne bisa addu\’o\’insu ga dorewar kasar nan da kuma addu\’o\’insu ga samun lafiyar maigidanta shugaba Muhammadu Buhari.
Sai ta hori musulmi da su kasance sun ci gaba da dabi\’un da watan azumin ya koyar da su na son juna da hadin kai da juriya da zamantakewa mai kyau da kauce wa fitintinu, wanda ta ce su ne abin da azumi yake koyarwa.
Mun sami wannan sanarwa daga, mai bai wa uwargidan shugaban kasa shawarwari kan harkokin yada labara  Adebisi Olumide Ajayi
(S.A Media wife of the President)

 

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here