Malaman Makarantar Firamare A Nijeriya Na Adawa Da \’Yancin Kananan Hukumomi

0
738

Rabo Haladu  Daga Kaduna

WASU jihohi  sun dauki tsawon watanni ba tare da biyar albashin ma\’aikata ba
Kungiyar Malaman makarantar \’Primary\’ ta Najeriya ta yi zanga-zanga tana neman a tsame ta daga yunkurin bai wa kananan hukumomi \’yancin cin gashin kai.
Mambobin kungiyar sun yi tattaki zuwa majalisar dokoki a jihar da kuma ofishin shugaban ma\’aikatan jihar domin mika kokensu.
Mukaddashin shugaban kungiyar reshen jihar, Kwamared Dalhatu AbduSalam Sumaila ya ce `ya`yan kungiyar za su shiga mawuyacin hali idan suka kasance a karkashin kananan hukumomi masu cin gashin-kansu.
Hakan a cewarsu zai faru ne idan aka yi la`akari da cewa a yanzu ma da wuya ake biyansu hakkokinsu, ciki har da albashi.
Malaman dai sun bukaci a bar su a karkashin gwamnatin tarayya ko ta jiha maimakon kananan hukumomi masu cin gashin kansu.
Shugaban ma\’aikata na jihar Kano, Alhaji Muhammad Auwal Na\’iya ya ce gwamnati za ta yi nazarin bukatar malaman makarantar.
Batun bai wa kananan hukumomi \’yancin cin gashin kai batu ne da ya dade yana janyo cece-kuce a Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here