Yau Lahadi Take Karamar Salla A Duniya

0
1021

Zubair A Sada, Mustapha Imrana Da Usman Nasidi

JIYA Asabar ne Mai alfarma sarkin musulmi Alhaji Sa\’ad Abubakar III ya bayar da umurnin a fara duban watan Shawwal da zai kawo karshen azumin watan Ramadan da musulmi a fadin duniyar nan suka azumci watan baki daya.

Sarkin musulmin ya bayar da wannan umurni ne kamar yadda aka saba, inda ya sanar da lambobin wayar wadansu mutane kimanin su 30 da za a iya tuntuba domin a sanar masu da ganin jinjirin watan.

To, cikin hukuncin Allah, jiya bayan sallar magariba kadan jama\’ar duniya suka ji sanarwa a kafafen yada labaru na duniya cewa, kasar Saudiyya da wasu kasashe bakwai ciki har da kasar Najeriya an ga watan na Shawwal, wanda ya kawo karshen azumin watan Ramadan na bana. Domin haka ne, yau Lahadi ta kama 1 ga wata, wato yau take salla karama a fadin duniya.

Wakilanmu na wannan jarida mai farin jini a sassan kasar nan za su aiko mana da yadda sallar ta kasance a matsayin goron salla in sha Allahu. A ci gaba da kasancewa tare da jaridar Gaskiya Ta Fi kwabo. A yi salla lafiya, muna taya musulmi barka da shan ruwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here